Sanatoci sun yi tutsu ga takwarorinsu dake kokarin tsige shugaban majalisar dattawa

Sanatoci sun yi tutsu ga takwarorinsu dake kokarin tsige shugaban majalisar dattawa

Majalisar dattawan Najeriya ta yi fatali da bukatar wasu yan tsiraru daga cikinsu na tsige shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan daga mukaminsa ta hanyar kada kuri’un amincewa, inji rahoton jaridar Sun.

A ranar Talata, 10 ga watan Disamba ne wata takarda ta bayyana a gaban majalisar dake dauke da sunayen Sanatoci guda 36 wadanda ke neman ganin an kada kuri’un amincewa ga Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisa.

KU KARANTA: Yansanda sun kama gawurtaccen barawon mutane a Gombe bayan ya amshi N9,000,000

Manufar wannan kuri’ar amincewa shi ne tabbatar da goyon baya ga shugaban, toh amma idan har wadanda basu amince da shi ba suka samu rinjaye, daga nan sai a kama hanyar tsige shi a daga mukaminsa. Sai dai wasu sanatoci sun yi mamakin yadda sunansu ya shiga cikin wannan jerin sunaye.

Wani sanata daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya, ya bayyana cewa: “Ban san dalilin da yasa masu bukatar ganin sun yi ma shugabancin majalisa kwalliya zasu saka sunana a cikinsu ba, bani da wata masaniya game wani bukatar kada kuri’ar amincewa.”

Sanatan ya kara da cewa manufar masu wannan shiri shi ne kwantar da hankulan Sanatoci game da son kai da shugaban majalisar ke nunawa wajen rabon ayyukan mazabu dake cikin kasafin kudin 2020.

“Abin tambayar a nan shi ne idan babu rami mai ya kawo rami, ina dalilin wani kuri’ar amincewa ga shugabancin majalisa a wannan lokaci? Duka duka kwanakinsu nawa? Ko dai sun tafka wani laifin ne daga watan Yunin 2019 da aka nada su zuwa yanzu da har suke bukatar goyon baya?” Inji shi.

Mataimakin bulaliyar majalisar,Sanata Abdullahi Sabi Aliu ya gabatar da kudurin dakatar da batun kada kuri’ar amincewar, sai dai bai bada wani dalilin yin haka ba, daga nan kumasa Sanata Philip Aduda ya goyi bayansa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tsohon gwamnan jahar Borno, Kashim Shettima ne ya gabatar da kudurin kada kuri’ar amincewar, kuma sunayen Sanatocin da yace suna goyon bayan kudurin sun hada da Danjuma Goje da Ali Ndume

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel