Majalisar sarakuna: Gwamnatin Kano ta yi martani a kan hukucin kotu

Majalisar sarakuna: Gwamnatin Kano ta yi martani a kan hukucin kotu

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani a kan hukuncin wucin gadi da wata babbar kotun jihar ta yanke a kan dokar kafa majalisar sarakunan jihar.

A wani jawabi mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labaran jihar, Malam Muhammad Garba, gwamnatin Kano ta ce hukuncin kotun bai shafi sabbin masarautun jihar da aka kirkira ba.

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa wata babbar kotun jihar Kano a karkashin Jastis Tijjani Bdamosi ta yanke hukuncin dakatar da gwamna Ganduje daga kafa majalisar sarakuna da kuma nada mambobin tare da tsayar da ranar 17 ga watan Disamba domin cigaba da sauraron karar.

A jawabin da gwamnatin ta fitar ranar Laraba, kwamishinan ya zargi makiya sabbin masarautun da aka kafa da sauya ma'anar hukuncin tare da bayyana cewa zasu sha kunya a karshe, bayan kotu ta yanke hukunci na karshe a kan batun.

Jawabin ya kara da cewa babu shakka bangaren gwamnati ne zai yi nasara a karshe saboda an bi doka wajen kirkirar sabbin dokokin masarautu a jihar Kano.

Kwamishinan ya bukaci jama'ar jihar Kano da su zauna lafiya tare da cigaba da yin biyayya ga doka a yayin da kotu ta zartar da hukunci.

Source: Legit

Online view pixel