Bayan garkame El-Zakzaky, kotu ta bada umurnin jefa yan Shi'a 60 gidan yari

Bayan garkame El-Zakzaky, kotu ta bada umurnin jefa yan Shi'a 60 gidan yari

Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bada umurnin garkame yan kungiyar mabiya akidar Shi'a 60 a gidan gyara halin Kuje Abuja da na Suleja, jihar Neja.

Yayinda kotun ta dawo zama ranar Talata, lauyan yan Shian, Mista Bala Dakum, ya sanar da kotun cewa yana bukatar kotn ta basu beli.

Amma sai kotun ta janyo hanlinsa cewa takardan beli daya kacal ya rubuta na bukatar belin mutane 60, maimakon takardu 60, daya ga kowani mai laifi, lauyan ya je zai janye.

Sai Alkali mai shari'a, Suleiman Belgore, yayi watsi da bukatar tunda lauyan yan Shi'an ya janye da kansa.

Sakamakon haka, lauyan gwamnati, Simon Lough, ya bukaci kotu ta bada umurnin garkame yan Shi'an a kurkukun Kuje da Suleja.

Ya bukaci a garkame mutane 54 a kurkukun Kuje, sannan a kai sauran shidan da suke mata a kurkukun Suleja, jihar Neja.

KU KARANTA: Ba zamu kara kiran Buhari shugaban kasa ba, Manjo Janar zamu rika kiransa - Jaridar Punch

Alkali yace: "A garkame munkaran a gidajen gyara hali. Za'a ajiyesu a gidajen gyara halin Kuje da Suleja. Za'a cigaba da sauraron karan a gidan gyaran Kuje."

Alkalin ya dage karar zuwa ranar 5 ga watan Febrairun 2020.

Jami'an hukumar yan sanda sun damke yan Shi'an 60 a ranar 22 ga Yuli bayan zanga-zangan da yayi sanadiyar mutuwar babban jami'in dan sanda DCP Usman Umar da mai bautan kasa, Precious Owolabi a birnin tarayya Abuja.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel