Kano: EFCC ta karbe Naira Miliyan 643.9 da Dala miliyan 706.8 a 2019

Kano: EFCC ta karbe Naira Miliyan 643.9 da Dala miliyan 706.8 a 2019

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta reshen yankin Kano ta bayyana cewa ta samu karba kudi Naira miliyan 643.942 a hannun Marasa gaskiya.

EFCC ta yi wannan jawabi ne ta bakin Mukaddashin shugabanta, Mista Ibrahim Magu, a Ranar Litinin, 11 ga Watan Disamban 2019. Mista Magu ya yi bayanin ne a ofishin hukumar da ke Kano.

Shugaban hukumar EFCC na shiyyar Kano, Akaninyene Eziman, shi ne ya wakilci Ibrahim Magu a wajen taron. Akaninyene Eziman ya bayyana duk abin da jami’ansu su ka karbe na kudi a bana.

A cewar Mista Akaninyene Eziman, EFCC ta gano Dala 706,800, da kuma kudin kasar Sin na Yen har 2, 800. Jami’an da ke yaki da rashin gaskiya sun kuma karbe Riyal 294, 950 na kudin sata.

Har ila yau, shugaban hukumar ya sanar da Duniya cewa sun samu korafi 495 daga bakin mutane, daga ciki an karbi 325, sannan an shigar da kara a gaban kotu domin ayi bincike kan korafi 100.

KU KARANTA: Tsofaffin Gwamnonin da EFCC ta ke zargi da sata kuma aka ji shiru

Kano: EFCC ta karbe Naira Miliyan 643.9 da Dala miliyan 706.8 a 2019

Jami'an EFCC sun samu tarin kudin sata a cikin shekara
Source: Facebook

Bugu da kari, EFCC ta yi dace wajen ganin an kama mutun 21 da laifi a yankin na Kano. An yi duk wannan ne daga farkon Watan Junairun bana zuwa Disamban nan inji Mista Ibrahim Magu.

Magu ya ce: “Yaki da rashin gaskiya aikin kowa ne a cikin mu domin fito da Najeriya daga halin kangi, don haka dole mu hadu mu rika bankado marasa kishi da ke neman kawo mana cikas.”

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta rahoto cewa shugaban hukumar yaki da cin hanci na Kano, Alhaji Muhyi Magaji da shugabannin hukumar kwadago sun yi jawabi a wajen taron.

Idan ba ku manta ba a shekaran jiyan ne aka yi bikin ranar yaki da rashin gaskiya na Duniya na wannan shekarar ta bana. An yi wa bikin shekarar 2019 da taken ‘Zero Tolerance to Corruption’.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel