Yanzu-yanzu: Gingimari ta murkushe motar tasi a Abuja

Yanzu-yanzu: Gingimari ta murkushe motar tasi a Abuja

An yi rashin wata mata yayinda wata gingimarin mota mai dauke da trakta ta murkushe motar tasi a unguwar Nyanya, babbar birnin tarayya Abuja. Punch ta ruwaito.

Hadarin ya auku ne misalin karfe 9:40 na safen nan inda gingimarin motar mai lamba KSB379XA (Kwara) ta bi ta kan motoci da dama, har da dan jaridan Punch.

Amma dan jaridan ya tsallake rijiya da baya ba tare da jin wani mugun rauni ba.

Wata mata dake zaune cikin motar tasi dake ajiye a bakin hanya kadai ta rasa rayuwarta inda ta cika a take.

An samu nasarar tsamo direban Tasin daga cikin motar da rai kuma an garzaya da shi asibiti.

An samu labarin cewa birkin gingimarin motar ne ya samu matsala a barikin Sojojin Mogadishu Cantoment da akafi sani 'Abacha Barracks'.

Tuni dai direban gingimarin ya arce daga wajen ya bar motarsa.

Jami'an hukumar kiyaye haduran kan hanyoyi da yan sanda sun isa wajen.

Yanzu-yanzu: Gingimari ta murkushe motar tasi a Abuja

Yanzu-yanzu: Gingimari ta murkushe motar tasi a Abuja
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel