Ba zamu kara kiran Buhari shugaban kasa ba, Manjo Janar zamu rika kiransa - Jaridar Punch

Ba zamu kara kiran Buhari shugaban kasa ba, Manjo Janar zamu rika kiransa - Jaridar Punch

Jaridar Punch ta bayyana cewa ba zata sake kiran shugaba Buhari da suna 'Shugaban kasa' ba, daga yanzu 'Manjo Janar' za ta rika amfani da shi wajen rubuta sunansa saboda kama-karyar da gwamnatinsa keyi.

A budaddiyar wasikar da jaridar ta wallafa kan shugaban kasan ranar Laraba, jaridar Punch ta ce ba zata sake kiran gwamnatin Buhari a matsayin 'gwamnati' ba, daga yanzu 'mulki' za ta rika kiran gwamnatinsa.

Jaridar tace: "A matsayin nuna rashin amincewarmu kan kama-karyan da akeyi, daga yanzu jaridar PUNCH za ta rika kira Buhari da sunansa na mulkin Soja, 'Manjo Janar' kuma gwamnatinsa matsayin 'mulki' har sai ya daina cin mutuncin dokar da yakeyi."

An dade ana sukar gwamnatin shugaba Buhari da kin bin umurnin kotu da kuma gudanar da ayyukansa tamkar mulkin Soja.

KU KARANTA: Rikici a fadar shugaban kasa: Ba zan sake lamunta rainin wayonka ba - Aisha Buhari tayi fito na fito da Garba Shehu

A watan Oktoban 2016, jami'an hukumar DSS sun dira gidajen wasu Alkalan Najeriya cikin dare kuma sukayi awon gaba da su.

Gwamnatin ta cigaba da tsare Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da Sambo Dasuki, duk da cewa kotuna daban-daban sun bada umurnin sakesu.

Hakazalika, tsohon dan takaran shugaban kasa, Omoyele Sowore, wanda hukumar DSS ta sake damkewa kwana daya bayan sakeshi kan kiran juyin-juya halin da yayi.

Bayan sa'ao'i 48 da sake kamashi, hukumar bata kaishi kotu ba duk da cewa dokar kasa ta ce bai hallata a tsare mutum sama da kwanaki biyu ba ba tare da umurnin kotu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel