Yanzu-yanzu: Garba Shehu ya daina biyayya ga Buhari - Aisha Buhari

Yanzu-yanzu: Garba Shehu ya daina biyayya ga Buhari - Aisha Buhari

Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, ta saki bama-baman kalamai kan mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Aisha ta bayyana cewa Garba Shehu maimakon maida hankali wajen biyayya da kare shugaban kasa wajen al'umma, ya maida hankali wajen biyayya ga wasu yan tsiraru da aka fi sani da miyagun fadar shugaban kasa.

Ta zargi Garba Shehu da kullawa iyalan shugaba Buhari sharruruka tare da yi mata zagon kasa iri-iri wanda ya kai ga yiwa yaransa sharri.

Aisha ta laburta cewa Garba Shehu ya yi tsayin daka domin ganin cewa an ci mutuncinta ta hanyar sallamar hadimanta kafin ta farga ta dakile hakan.

Ta ce lallai Garba Shehu ya koma biyayya ga Mamman Daura maimakon shugaba Buhari.

Aisha tace: "Cigaban Najeriya na jingine da aiwatar da ayyukan ma'aikatan gwamnatin kamar yadda aka umurcesu, saboda su zama abin koyi ga al'umma."

"Ba abu mai kyau bane a ce ma'aikata su ajiye ayyukansu kuma su dauke hankalinsu. A matsayinsa na mai magana da yawun shugaban kasa, ai babban aikinsa shine kare mutuncin shugaban kasa da kuma tallata irin ayyukan kwarai da yakeyi aiwatarwa."

"Amma maimakon yin hakan, ya dauke biyayyarsa daga shugaban kasa zuwa ga wasu da basu da wani ruwa da tsaki kan yarjejeniyar da shugaban kasa yai da yan Najeriya a ranar 29 ga Mayun shekarun 2015 da 2019."

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel