Kano: Masu nada sarakuna sun maka Ganduje a kotu

Kano: Masu nada sarakuna sun maka Ganduje a kotu

- Majalisar nadin sarautar jihar Kano ta shigar da kara a gaban wata babbar kotun jihar

- Majalisar ta bukaci kotun da ta dakatar da Ganduje daga rantsar da majalisar sarakuna ta jihar

- Sun kara da rokar kotun da ta hana Gwamnan jihar Kano tube rawanin Sarki Sanusi Lamido

Majalisar nadin sarautar jihar Kano ta shigar da kara a gaban wata babbar kotun jihar Kano. Majalisar na bukatar hukunci ne da zai hana Gwamna Abdullahi Ganduje rantsar da sarakunan gargajiya a jihar.

A karar, majalisar nadin sararutar ta yi kira ga kotun da ta hana masu sararutar gargajiyan wanda suka hada da majalisar sarakunan yin hakan. Ta haramta musu nadin kamar yadda sabuwar dokar masarautun jihar Kano din ta shekarar 2019 ta basu dama.

DUBA WANNAN: Har yanzu ba mu shaida naɗin Sanusi ba - Masarautar

Masu nadin sarautar wadanda suka samu shugabancin Yusuf Nabahani (Madakin Kano) ya jawo hankalin kotun zuwa ga karar da take kalubalantar Gwamna Ganduje da kirkirar sabbin masarautu hudu a jihar.

Sun roki kotun da ta hana Ganduje rantsar da sabuwar majalisar nadin sarakunan har zuwa lokacin da shari’ar zata kammala.

Sun kara da rokar kotun da ta hana Gwamnan jihar Kano tube rawanin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II. Sun kara da bukatar kotun da ta hana sarkin shugabantar rantsar da sabuwar majalisar da kuma taron farko na majalisar sarakunan jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel