Ministan Buhari ya janye takararsa ta Sanata da kotu ta ce a sake zabe

Ministan Buhari ya janye takararsa ta Sanata da kotu ta ce a sake zabe

Tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa kuma Ministan harkokin yankin Neja Delta, Godswill Akpabio ya janye takararsa daga zaben raba gardama da ake shirin yi a mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso gabas.

A cikin wasikar da ya aike wa shugaban jam'iyyar ruling All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa, Adams Oshiomhole mai dauke da kwanan wata 2 ga watan Disamban 2019, Akpabio ya ce a matsayinsa na Ministan harkokin Neja Delta akwai muhimmin aiki da aka daura masa.

Ya ce ba zai iya watsi da muhimmin aikin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bashi ba don sake yin zaben raba gardama.

DUBA WANNAN: Har yanzu ba mu shaida naɗin Sanusi ba - Masarautar Kano

Ya umurci jam'iyyar ta APC ta rubuta wa Hukumar zabe mai zaman kanta INEC wasika kamar yadda sashi na 33 da 35 na dokar zabe na 2010 ya tanada su bayar da sunan wanda zai maye gurbinsa a zaben na raba gardama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel