Dalilin da yasa Najeriya ba za ta iya dena cin bashi ba - Ministan Kudi, Zainab

Dalilin da yasa Najeriya ba za ta iya dena cin bashi ba - Ministan Kudi, Zainab

Ministocin Kudi, Zainab Ahmed; Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; Karamin Ministan Sufuri, Gbemisola Saraki da Direktan Ofishin Bashi (DMO), Patience Oniha sun bayyana dalilan da yasa gwamnatin Najeriya ke karbar bashi.

Daily Trust ta ruwaito sun bayyana cewa ya zama dole gwamnati ta cigaba da karbo bashi domin gudanar da ayyukan da al'umma ke bukata tare da cewa ya zama dole a cigaba da karbar bashin.

Sun bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da suka gana da kwamitin majalisar dokoki na tarayya kan bashi da tallafi domin kare bukatar karbo bashi na $22.718 biliyan da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatarwa Majalisar Dattawa.

DUBA WANNAN: Cike da alfahari: Hotunan Buhari da Hanan bayan ta kammala digiri da sakamako mafi daraja

A yayin jawabin da ta gabatarwa majalisar, Ministan Kudi, Zainab Ahmed ta ce akwai bukatar karbo bashin domin gwamnati ta samu damar aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin 2020 don yi wa al'umma ayyuka da samar da ayyukan yi.

"Ya zama dole mu gina titunan mota da na jirgin kasa idan har muna son mu habbaka tattalin arzikin mu. Ayyukan gin al'umma kawai za a yi da kudaden. Ya zama dole mu cike gibin da muke da shi yanzu. Mun san cewa akwai ka'idojin da za mu kiyaye.

Misis Ahmed ta ce ba abinda damuwa bane bashin inda ta ce, "Najeriya ba ta da matsalar rashin biyan bashi sai dai ta rashin inganta karbar kudaden shiga. "Za muyi amfani da dukkan kudaden ta hanyoyin da suka dace."

A bangarensa, Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya ce ba zai yi wu gwamnati ta yi watsi da ayyukan gine-gine da kasar ke bukata ba domin su ke inganta cigaban kasar.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel