Kogi: ‘Yan Sanda sun cafke wadanda ake zargi da laifin kashe Salome Abuh

Kogi: ‘Yan Sanda sun cafke wadanda ake zargi da laifin kashe Salome Abuh

Mun samu labari cewa Rundunar Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya sun yi nasarar kama wasu mutane da ake zargin akwai hannunsu wajen hallaka Shugabar mata ta jam’iyyar PDP kwanaki.

Idan ba ku manta ba, wasu ‘yan bangar siyasa sun hallaka Misis Salome Abuh, wanda Jagora ce ta jam’iyyar PDP a karamar hukumar Ofu a jihar Kogi. Hakan ya faru ne a lokacin zaben gwamna.

Wadannan Miyagun mutane sun bi Salome Abuh zuwa gidanta ne, inda su ka kona ta har lahira a rikicin siyasar da ya barke a sa’ilin da ake gudanar da zaben 16 ga Watan Nuwamban 2019 a jihar.

Yanzu Dakarun ‘Yan sanda sun yi ram da wasu mutanen da ake zargin cewa su ne su ka ga bayan wannan Baiwar Allah. Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Kogi, Hakeem Busari, ya bayyana haka.

KU KARANTA: Sanatan PDP Dino ya yi maganan bayan nasarar APC a Kogi

Kogi: ‘Yan Sanda sun cafke wadanda ake zargi da laifin kashe Salome Abuh

Wasu mugaye sun kashe Jagorar Matar PDP a Jihar Kogi
Source: Facebook

Bayan ‘namijin lalube’, binciken Yan sanda ya kai ga mutum shida da ake kyautatata zaton su ne su ka yi taron gwiwa su ka kashe wannan ‘yar siyasa. CP Hakeem Busari ya shaidawa ‘yan jarida.

Ocholi Edicha, shi ne uban wannan gayya da ake zargi, inda ya jagoranci sauran ‘yan uwansa su ka kona ‘Yar adawar kurmus. A cikin karshen makon jiya ne aka bizne Acheju Salome Abuh.

‘Yan daban sun bi Jagorar hamayyar da gidanta ya ke Yankin Ochadamu, a Garin Ofu su ka kashe ta haka-kawai ana tsakiyar ruguntsumin zabe. Bayan ita akwai wasu da aka kashe a lokacin.

Wannan ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni ga jami’an ‘yan sanda su yi maza su bankado wadanda su ka yi wannan ta'adi. Ana sa ran cewa nan gaba za a maka su a gaban kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel