Fayose ya nemi afuwar 'yan jam'iyyar PDP kan abinda ya aikata a baya

Fayose ya nemi afuwar 'yan jam'iyyar PDP kan abinda ya aikata a baya

A ranar Talata ne tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi kira ga mambobin jam'iyyar PDP, reshen jihar wadanda ransu ya baci da shi a kan su yafe mishi.

Fayose, wanda ya yi wannan jawabin a wani taron zaman lafiya da mambobin jam'iyyar na dukkan kananan hukumomin jihar, ya yi kira garesu da su mayar da komai ba komai ba.

Ya roki gafarar wadanda suka fusata dashi, wadanda yace akwai yuwu ya taba bata musu rai.

Kamar yadda yace, dole ne jam'iyyar PDP ta yi gyare-gyare tare da shirin zaben nan gaba a jihar. Akwai bukatar sadaukarwa mai yawa daga mambobin a jihar.

DUBA WANNAN: Cike da alfahari: Hotunan Buhari da Hanan bayan ta kammala digiri da sakamako mafi daraja

"Muna kokarin kawo sauyi a jam'iyyarmu saboda muna bukatar sabbin tsare-tsare a jam'iyyar. Dole ne sanar wa juna gaskiya. Kuma mu hada kanmu don samun tsinana abu nagari.

"Nasan wasu na fushi dani kuma na fahimci cewa dukkaninmu mutane ne. Ina neman afuwa daga dukkanmu don mu mutane ne.

"Ya dace mu zo mu hada hannu wuri daya domin mu gina jam'iyyar mu a jihar nan kada jamiyyar ta rushe. Wannan shine abinda na sa gaba a matsayina na jagora.

"Na yi hakan ne shekara guda bayan na sauka daga mulki saboda in bawa jamiyyar AC dama ta nuna wa alumma abinda za ta iya tubukawa kuma kowa ya ga abinda ta yi.

"Ba na zo nan da wata manufa na daban bane sai dai kawai bana so jam'iyyar mu ta sha kaye," a cewar Fayose.

Tsohon gwamnan kuma ya yi amfani da damar wurin taya Sanata Biodun Olujumi murna kan nasarar da ta samu a matsayin 'yar majalisa mai wakiltan mazbaar Ekiti South inda ya ce har yanzu ita jogora ce a jam'iyyar a jihar.

Ya ce, "Bani da wata matsala da ita kuma ina neman afuwarta kan abinda ya faru a baya. Ina taya ta murna (Olujumi) kan nasarar da ta samu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel