Yansanda sun kama gawurtaccen barawon mutane a Gombe bayan ya amshi N9,000,000

Yansanda sun kama gawurtaccen barawon mutane a Gombe bayan ya amshi N9,000,000

Rundunar Yansandan jahar Gombe ta yi nasarar kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, matashi dan shekara 20, Yusu Umar tare da abokin ta’asarsa, Nasiru Hassan dan shekara 28, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin Yansandan jahar, SP Mary Malum ce ta tabbatar da kama miyagun mutanen a ranar Talata, 10 ga watan Disamba yayin da take gabatar dasu ga manema labaru a babban ofishin rundunar Yansandan jahar.

KU KARANTA: Tabdijam! Hisbah ta saki yan daudu guda 30 bayan sun yi sallar dare raka’a 40

Yansanda sun kama gawurtaccen barawon mutane a Gombe bayan ya amshi N9,000,000

Masu garkuwa a Gombe
Source: Facebook

“Miyagun sun yi ma wani mutumi Alhaji Abubakar Mohammed mai shekaru 72 fashi ne, inda suka kwace masa N200,000 sa’annan kuma suka yi awon gaba da shi daga gidansa dake unguwar Yelwa a Dadin Kowa zuwa tsaunin Dukul cikin karamar hukumar Kwami.

“Miyagun sun cigaba da rike Alhaji Abubakar tsawon kwanaki 19, har sai da aka biyasu kudin fansa naira miliyan 9 sa’annan suka sake shi. Amma da yake Yansanda sun cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin tare da tattara bayanai, daga bisani mun kamasu a unguwar Keandon Liji cikin karamar hukumar Yamaltu Deba.

“Kuma dukkaninsu sun amsa hannunsu cikin satar mutum da yi masa fashi, da kuma amsan kudin fansa, mun kamasu da wayoyin salula guda biyu, zamu gurfanar dasu gaban kotu da zarar mun kammala gudanar da bincike a kansu.” Inji ta.

A hannu guda kuma, Yansandan Gombe sun kama Saleh Usman da Abdullahi Dangwamna da laifin fashi da makami da garkuwa mutane bayan sun yi ma Fasto Husseini Umar fashin kudi N600,000 sa’annan suka amshi kudin fansa naira miliyan 6 kafin suka sako shi.

Sai dai kaakaki Mary tace akwai abokan ta’asansu guda hudu, Lawan Boda, Babangida, Iro da Niga wanda a yanzu sun cika wandonsu da iska, inda ta tabbatar da cewa Yansanda na iya kokarinsu don kamo su, domin su fuskanci hukunci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel