Gwamna Zulum ya sallami Malamai 200 da ba sa zuwa aiki a jahar Borno

Gwamna Zulum ya sallami Malamai 200 da ba sa zuwa aiki a jahar Borno

Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum ya bada umarnin dakatar da wasu malaman firamari 200 da ya kamasu da laifin kin zuwa wurin aikinsu a karamar hukumar Bama, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya bayyana cewa wadannan malamai 200 sun kwashe tsawon shekara daya cur basa zuwa makaranta domin koyar da dalibai, wanda shi ne aikin da aka daukesu yi.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Barayi sun afka gidan gwamnatin Bayelsa, sun sace naira miliyan 3.5

Gwamna Zulum ya kai ziyara karamar hukumar Kala Balge na jahar Borno wanda ruwa ya karya musu gada tsawon watanni 4 kenan, inda ya raba ma jama’an yankin tallafin kayayyaki daban daban a garin Rann, da sauran garuruwan da suka yi iyaka da kasar Kamaru.

Daga nan ne gwamnan ya zarce garin Bama inda ya kwana, washegari Litinin kuma ya shiga aikin zagayen makarantun garin, a yayin wannan rangadi ne gwamnan ya gano malaman dake kin zuwa aiki a makarantun firamari guda 8.

“Makasudin ziyarar dana kai Bama shi ne don rabon kayan tallafi ga yan gudun hijira da suka koma gida, zuwa yanzu mun raba kayan tallafi ga akalla mutane 12000, daga nan kuma mun zagaya makarantun firamari guda 8, inda muka gano daga cikin malamai 300 dake koyarwa a makarantu, 100 ne kawai suke zuwa aiki.

“Kusan guda 200 basa zuwa aiki kwata kwata, mun bincika mun gano fiye da shekara daya kenan basa zuwa aiki, don haka gwamnati za ta sallamesu daga aiki, kuma zamu dauki sabbin malamai da zasu maye gurbinsu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wasu gungun barayi sun afka cikin gidan gwamnatin jahar Bayelsa dake Yenagoa, babban birnin jahar a ranar Talata inda suka yi awon gaban da makudan kudi da suka kai naira miliyan 3.5.

Mataimakiyar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar, Ebizi Ndiomu-Brown wanda aka sace kudin daga ofishinta ce ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace N3.5m aka sace ba miliyan 40 kamar yadda wasu yadawa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel