Masu garkuwa da sun yi awon gaba da darakta, shugaban sakandari da wasu mutane 3 a Yola

Masu garkuwa da sun yi awon gaba da darakta, shugaban sakandari da wasu mutane 3 a Yola

Gungun wasu miyagu yan bindiga sun kai wata mummunar farmaki a garin Yolan jahar Adamawa inda suka yi awon gaba da wani babban jami’in gwamnati mai mukamin darakta a ma’aikatar shari’a ta jahar Adamawa, Samuel Yaumande.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito a daren Litinin, 9 ga watan Disamba ne yan bindigan suka kai farmaki gidan daraktan dake unguwar Sangere, cikin birnin Yola inda suka dauke shi.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Barayi sun afka gidan gwamnatin Bayelsa, sun sace naira miliyan 3.5

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya ga wannan jami’in gwamnatin, yan bindigan sun dauke wani shugaban makarantar sakandari, tare da wasu mutane uku, duk a yayin wannan samame da suka kai.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace tuni sun aika da tawagar Yansanda don bin sawun yan bindigan tare da ceto mutanen.

Jahar Adamawa na cigaba da samun yawaitan sace sacen mutane duk kuwa da cewa rundunar Yansandan jahar tana kama barayin mutane sosai, don kuwa ko makon data gabata sai da rundunar ta bayyana wasu masu garkuwa da mutane su 106 da ta kama.

A wani labari kuma, wasu gungun yan bindiga dadi da ba’a san ko su wanene ba sun kaddamar da farmaki a jami’ar jahar Kogi dake garin Ayingba na jahar Kogi, inda suka kashe wani dalibin jami’a dan ajin karshe.

Yan binidigan sun daidaici daidai lokacin da dalibin yake zana jarabawa ne a sashin ilimin aikin banki da kudade na jami’ar, inda yake zana jarabawarsa ta karshe a jami’ar, suka dirka masa bindiga, kuma ya mutu nan take.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, rundunar Yansandan jahar Kogi ko hukumar makarantar basu tabbatar da aukuwar lamarin ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel