Shugaba Buhari ya dira Masar (Bidiyo, Hotuna)

Shugaba Buhari ya dira Masar (Bidiyo, Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Aswan, kasar Masar da daren Talata, 10 ga watan Disamba, 2019.

Buhari ya isa Masar ne domin halartan taron zaman lafiya da cigaban nahiyar Afirka ne da shugaban kasar Misra, AbdulFatah El-Sisi ya kirkiro a matsayinsa na shugaban gamayyar kasashen Afrika AU.

Taron, wanda za'a fara ranar 11 ga watan Disamba, 2019, zai tattauna a kan alakar da ke tsakanin zaman lafiya da cigaba a nahiyar Afrika da kuma yadda za a samar da hanyoyin karfafa dokokin da zasu tabbatar da tsaro tare da kawo cigaban kasashen nahiyar Afrika.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, takwaransa na jihar Edo, Godwin Obaseki, da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Sauran ragowar 'yan tawagar shugaba Buhari sun hada da; Ministan tsaro, Bashir Magashi, karamin ministan harkokin kasashen ketare, Zubairu Dada, mai bawa shugaba kasa shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, da kuma babban darektan hukumar leken aisri ta kasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel