'Yan bindiga sun yi garkuwa da darakta, Shugaban makaranta da wasu mutane 3 a Adamawa

'Yan bindiga sun yi garkuwa da darakta, Shugaban makaranta da wasu mutane 3 a Adamawa

Wasu 'yan bindiga sun sace daraktan hukumar aikin gwamnati na jihar Adamawa, Samuel Yaumande, Shugaban wata makaranta da kuma wasu mutane biyu.

Kamar yadda wata majiya ta sanar da jaridar Daily Trust, 'yan bindigar dauke da makamai sun kutsa gidan daraktan ne da ke yankin Sangere a jihar Yola, da misalin karfe 11:30 na Daren Litinin. Tuni suka yi awon gaba da shi tare da wasu makwabtansa uku.

Garkuwa da mutane a koyaushe karuwa yake yi a jihar a cikin shekarun nan. Duk da an kama daruruwan mutane da ake zargi da wannan aika-aikar.

A makonni uku da suka gabat, jami'an 'yan sanda sun kai samame inda suka kwashe wadanda ake zargi da garkuwa da mutane har 106.

DUBA WANNAN: Jami'ar Bayero ta Kano ta kara kudin makaranta, ta bayyana dalilanta

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje ne ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an baza wasu jami'an tsaro an yankin don gano wadanda suka yi garkuwar tare da samo wadanda ka yi garkuwa dasu.

"Mun samu rahoton cewa, anyi garkuwa da daraktan ma'aikatar shari'a. Har ila yau, mun gano cewa anyi garkuwa da wasu mutane uku. Mun tura jami'anmu karkashin rundunar 'Operation Farauta' don bincikar yankin. A halin yanzu an gurfanar da masu garkuwa da mutanen da suka shiga hannu," Nguroje ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel