Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa za ta canja wa Kwallejin Fasaha da ke Daura suna

Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa za ta canja wa Kwallejin Fasaha da ke Daura suna

Bukatar sauyawa Kwallejin Fasaha na tarayya da ke Daura suna ta samu wuce karatu na biyu a Majalisar Dattijai. An yi hakan ne don tunawa da marigayi Sanata Mustapha Bukar.

Marigayi Sanata Mutapha Bukar ya wakilci Katsina ta Arewa a majalisar dattijai karo ta takwas kuma shine ya jagoranci bukatar kafa Kwallejin Fasahar ta tarayyar da ke Daura a jihar Katsina.

Wanda ya gaji Bukar a majalisar dattijai, Sanata Ahmed Babba Kaita ne ya mika bukatar sauyin sunan babbar makarantar.

Kamar yadda takardar da Mohammed Isa, mataimaki na musamman ga Shugaban majalisar dattijai ya fitar, yace Sanatocin sun dau lokaci suna makoki tare da tuno lokutan da suka yi zaman arziki tare da abokin aikin nasu a majalisar dattijan yayin rayuwarsa.

DUBA WANNAN: Har yanzu ba mu shaida naɗin Sanusi ba - Masarautar Kano

Dukkannin kakakin majalisar sun bada goyon bayan wannan bukatar ta tunawa da Bukar. Sun bayyana cewa hakan zai zama tamkar karin kwarin guiwa ga wadanda suka rike kujerun siyasa don su kafa tarihi.

A yayin mika godiya ga Kaita da ya mika bukatar gaban majalisar dattijan, Shugaban majalisar yace "wannan babban darasi ne ga 'yan siyasa a kan irin halayyar da ya dace su dinga bayyanawa. Ana kallonmu a matsayin mutanen banza saboda mutane basu fahimtarmu duk da sun yarda damu ne har suka zabe mu. A wannan lokacin, muna son kafa tarihi mai kyau kuma mu tabbatarwa mutanen da muke wakilta sun san hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel