Kano: Kotu tsayar da ranar yanke hukunci kan karar da Sanusi ya shigar game da Hukumar yaki da rashawa

Kano: Kotu tsayar da ranar yanke hukunci kan karar da Sanusi ya shigar game da Hukumar yaki da rashawa

- Kotun tarayya a Kano ta tsayar da ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2020 don yanke hukunci kan karar da Sanusi ya shigar

- Mai martaba Sarkin Kano, Sanusi II ya yi karar hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano bayan ta zarge shi da bannatar da N3.4bn kuma ta nemi a dakatar da shi

- Lauya mai kare Sanusi, Saida Suraj ya ce hukumar yaki da rashawar ba ta bawa Sarkin damar ya kare kansa ba

Wata babban kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta tsayar da ranar 20 ga watan Fabrairun 2020 domin yanke hukunci kan karar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shigar kan Hukumar sauraran korafin jama'a da yaki da rashawa na jihar Kano.

A rahoton da hukumar ta bayar kan yadda ake kashe kudaden masarautar Kano ta bayar da shawarar da dakatar da Sarki Sanusi kan zarginsa da almubarazanci da kudaden masarautar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Hukumar ta ce ta gano cewa an barnatar da naira biliyan 3.4 karkashin mulkin Sanusi tsakanin 2014 zuwa 2017.

Sai dai, lauyan Sanusi, Saida Suraj, ya bukaci kotu ta tabbatarwa wanda ya ke karewa hakokinsa na dan adam inda ya ce hukumar ta bayar da rahoto kan sarkin ne amma ba ta bashi damar ya kare kansa ba.

DUBA WANNAN: Yadda wani sanata ya wawure kudin aikin mazabarsa ya gina otel - ICPC

A bangarensa lauyan hukumar yaki da rashawar ta jihar Kano, Sylvester Shikyil ya yi martani inda ya ce karar ba ta hakkin dan adam bane inda ya ce hukumar tana bincike ne bisa karfin ikon da doka ya ba ta.

Ya bayyana cewa amsa tambayoyin da wani Munnir Sanusi ya yi a madadin sarkin bai wadatar ba inda ya ce kotun ma ba ta da ikon sauraron karar domin kotun ma'aikatu na kasa ce kawai ke da ta cewa a kan batun.

Bayan sauraron bangarorin biyu, alkalin kotun, Obiorah Egwuatu ya dage cigaba da sauraron shari'ar kuma ya tsayar da ranar 20 ga watan Fabrairun 2020 a matsayin ranar da za a yanke hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel