An sake kwatawa: Barayi sun afka gidan gwamnatin Bayelsa, sun sace naira miliyan 3.5

An sake kwatawa: Barayi sun afka gidan gwamnatin Bayelsa, sun sace naira miliyan 3.5

Wasu gungun barayi sun afka cikin gidan gwamnatin jahar Bayelsa dake Yenagoa, babban birnin jahar a ranar Talata inda suka yi awon gaban da makudan kudi da suka kai naira miliyan 3.5, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mataimakiyar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar, Ebizi Ndiomu-Brown wanda aka sace kudin daga ofishinta ce ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace N3.5m aka sace ba miliyan 40 kamar yadda wasu yadawa ba.

KU KARANTA: ‘Dan Zakzaky ya bayyana damuwarsa da halin da iyayensa za su shiga a kurkukun Kaduna

Sai dai tace bata da wani a rai da take tunanin shi ya sace kudin, sai dai kowa ma zai iya daukan wadannan kudade, don haka tace ta bari kawai har sai rundunar Yansanda ta kammala gudanar da bincikenta.

Shi ma kaakakin rundunar Yansandan jahar Bayelsa, Asinim Butswat ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace tabbas an fasa ofishin Brown a lokacin da ta tafi aiki a wajen jahar Bayelsa aka sace N3.5 bayan an balle kofarta, sa’annan aka fasa ma’ajiyar kudin dake ofishinta.

Kaakakin yace da fari sun kama Yansanda 3, jami’an civil defence guda 4 da kuma wani ma’aikaci a ofishin gwamna, inda aka gudanar da bincike a kansu, amma daga bisani aka sakesu, inda tuni suka koma bakin aikinsu.

A wani labarin kuma, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa akwai almundahana a yadda tsohuwar gwamnatin shugaba Jonathan ta cefanar da kamfanin wutar lantarkin Najeriya a shekarar 2013.

Sanata Ahmad Lawan ya bayyana haka ne yayin da yake bude taron tattauna a kan matsalar wutar lantarki wanda kwamitin wutar wutar lantarki na majalisar dattawa ta shirya, inda ya yi kira ga gwamnatin Buhari ta kaddamar da dokar ta baci a sha’anin wuta a Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel