Yan bindiga sun bindige dalibin jami’a yayin da yake zana jarabawa a jahar Kogi

Yan bindiga sun bindige dalibin jami’a yayin da yake zana jarabawa a jahar Kogi

Wasu gungun yan bindiga dadi da ba’a san ko su wanene ba sun kaddamar da farmaki a jami’ar jahar Kogi dake garin Ayingba na jahar Kogi, inda suka kashe wani dalibin jami’a dan ajin karshe.

Jaridar Daily Times ta ruwaito yan binidigan sun daidaici daidai lokacin da dalibin yake zana jarabawa ne a sashin ilimin aikin banki da kudade na jami’ar, inda yake zana jarabawarsa ta karshe a jami’ar, suka dirka masa bindiga, kuma ya mutu nan take.

KU KARANTA: ‘Dan Zakzaky ya bayyana damuwarsa da halin da iyayensa za su shiga a kurkukun Kaduna

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, rundunar Yansandan jahar Kogi ko hukumar makarantar basu tabbatar da aukuwar lamarin ba.

A hannu guda kuma, wani dan bindiga dadi ya kaddamar da harin mai kan uwa da wabi a wani asibitin kasar Czech Republic, inda a dalilin haka ya halaka akalla mutane shida, tare da jikkata wasu da dama.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata a wani asibiti dake birnin Ostrava, cikin yankin Arewa maso gabashin kasar Czech Republic. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa dan bindigan ya ranta ana kare.

“An kwashe duk jama’an dake cikin asibitin, amma har yanzu Yansanda suna farautar mutumin daya aikata laifin.” Inji Yansanda.

Sai dai daga karshe jami’an Yansandan kasar Czech Republic sun samu nasarar cimma wannan dan bindiga, amma ko kafin su kai ga kama shi har ya dirka ma kansa bindiga, ya kashe kansa da kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel