Kaduna: Mun samu korafi 580, mun sa an garkame mutum 27 a 2019 - EFCC

Kaduna: Mun samu korafi 580, mun sa an garkame mutum 27 a 2019 - EFCC

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta reshen jihar Kaduna, ta bayyana cewa ta karbi korafi daga jama’a da kungiyoyi fiye da 580 a shekarar nan.

Shugaban hukumar na reshen Kaduna, Mailafiya Yakubu, ya bayyana wannan a lokacin da hukumar ta shirya wani tattaki na musamman domin tunawa da ranar yaki da cin hancin bana.

A cewar Mailafiya Yakubu, korafi fiye da 580 ya shigo hannunsu daga Watan Junairun 2019 kawo yanzu. Mailafiya ya yi wannan jawabi ne a Ranar Litinin, 9 ga Watan Disamban 2019 a Kaduna.

Mista Mailafiya ya kuma shaidawa Duniya cewa akwai shari’a fiye da 100 da yanzu ake yi a kotu daban-daban. Daga cikin wadannan shari’a ne aka yi nasarar kama mutane 27 da laifi a shiyyar.

KU KARANTA: AMCON: Katutun bashi ya sa an karbe kamfanin Jide Omokore

“Bayan haka kuma, mun samu damar fara karbe gidaje 15 da aka mallaka ta muguwar hanya kafin a kammala shari’a, kuma mu na kokarin ganin an bamu damar karbe gidajen har abada.”

“Samun korafi sama da 580 a watanni 11 ya nuna yadda jama’a su ka yi amanna da EFCC. Ko ma dai ya ne, mun yi nasarar kama wasu mutane da laifi, kuma har yanzu ana cigaba da hakan.”

“Za mu cigaba da kama mutane mu na gurfanar da su a gaban kotu. Har a Ranar bikin Kirismeti.” Shugaban na EFCC ya kuma kara da cewa Naira miliyan 300 aka tsinto daga abin da aka yi bari.

“Mu na so Jama’a su san satar dukiyar al’umma mummunan abu ne, sharri ne kuma mai hadari. Dole Jama’a su bada gudumuwa. Ina farin ciki da mutane su ke goyon bayanmu.” Inji EFCC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel