Abin kunya: 'Yan sanda sun kama jami'in hukumar 'shige da fice' da ke safarar makamai ga 'yan bindiga a Sokoto

Abin kunya: 'Yan sanda sun kama jami'in hukumar 'shige da fice' da ke safarar makamai ga 'yan bindiga a Sokoto

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Sokoto ta kama wani babban jami'i mai mukamin insifekta a hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) da laifin safarar alburusai ga 'yan bindiga a jihar Sokoto.

Asirin ma'aikacin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya tonu ne biyo bayan bayanan da wasu 'yan bindiga da aka kama kwanan nan suka bayar.

Jami'in da ake zargin yana rike da wata karamar hukuma a jihar Sokoto da ta sha fama da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin bayan bayan nan.

Da aka tuntubi kakakin hukumar NIS, Bello Ahmad, ya ce ba zai yi magana a kan lamarin ba saboda rundunar 'yan sanda tana gudanar da bincike a kai.

Sai dai, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Sokoto, ASP Abdulkadir Datti, ya tabbatar da kamun tare da bayyana cewa har yanzu suna gudanar da bincike a kan jami'in.

A kwanakin baya ne hukumar bayar da agajin gagga wa a ta jihar Sokoto (SEMA) ta bayyana cewa hare - haren 'yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 200 tare da raba wasu mutanen 45,175 da muhallinsu a daga watan Yuli na shekarar 2018 zuwa yanzu.

Abin kunya: 'Yan sanda sun kama jami'in hukumar 'shige da fice' da ke safarar makamai ga 'yan bindiga a Sokoto

Shugaban hukumar NIS; Muhammad Babandede
Source: UGC

SEMA ta kara da cewa an lalata kauyuka da garuruwa 66 yayin da aka lalata kasar noma da fadinta ya kai hekta 21,316, lamarin da ya shafi harkar noma a kananan hukumomi biyar na jihar.

DUBA WANNAN: Kisan kishiya da 'ya'yanta 7: Kotu ta yanke wa matar aure hukuncin kisa

Lamarin ya shafi kananan hukumomin Tangaza, Rabah, Isa, Sabon Birni da Tureta.

Sai dai, yanzu za a iya cewa lamarin ya lafa tun bayan fara tattauna da niyyar yin sulhu da 'yan bindigar.

A cewar kwamishinan harkokin tsaro a jihar Sokoto, Kanal Garba Moyi (mai ritaya), sun tattauna tare da yin sulhu da a kalla kungiyoyin 'yan bindiga 17 tare da bayyana cewa, "ya zuwa yanzu mun samu nasarar karbar bindiga fiye da 100 daga hannunsu kuma muna cigaba da tattauna da su da karbar karin wasu makaman."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel