Neman mafita: Majalisar sarakunan Arewa ta gudanar da muhimmin taro a Kaduna

Neman mafita: Majalisar sarakunan Arewa ta gudanar da muhimmin taro a Kaduna

Majalisar Sarakunan gargajiya ta Arewa ta yi taronta karo na shida a jiya a garin Kaduna. Majalisar ta tattauna ne a kan manyan kalubalen da ke fuskantar ba Arewa kadai ba, harda dukkan kasar baki daya.

Shugaban majalisar sarakunan Arewa kuma Sarkin Sokoto, Alhaji Sa'ad Abubakar yayin jawabinsa, ya ce daidaituwar kasar nan shine babban burinsu.

A yayin tabbatarwa da dukkan matakan gwamnati na cewa sarakunan gargajiyar abokan cigabansu ne, ya tabbatar da cewa "zamu cigaba da ba wa gwamnati shawara a kan abubuwan da ya kamata ta yi kuma mun tabbatar da cewa gwamnatin zata sauraremu."

Neman mafita: Majalisar sarakunan Arewa ta gudanar da muhimmin taro a Kaduna

Neman mafita: Majalisar sarakunan Arewa ta gudanar da muhimmin taro a Kaduna
Source: Depositphotos

Ya tabbatarwa da gwamnati cewa, masarautun gargajiyar basu yakar su, tare da tabbatar da cewa "masarautunmu na da hadin guiwa da gwamnati kuma masu ruwa da tsaki ne a kowanne mataki na gwamnati".

DUBA WANNAN: FIRS: Fowler ya gode wa Buhari, ya 'sace' gwuiwar masu cewa an cire shi

Ya kara da tunatar da shuwagabannin a kan bukatar su na mayar da hankali wajen shawo kan kalubalen da ke addabar kasar nan. Yace, "muna tabbatar wa da gwamnoninmu cewa zamu goyi bayansu idan bukatar hakan ta taso. Zamu yi matukar kokarinmu wajen tabbatar da cewa sun kammala shirye-shiryensu,

"Zamu cigaba da kira ga 'yan siyasa, zamu yi musu nasiha da su ji tsoron Allah," ya kara da cewa.

A bangaren Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, wanda mataimakiyarsa Dr Hadiza Balarabe ta wakilta, ya yi kira ga masarautun gargajiyan da su cigaba da taka rawa wajen hada kan al'umma tare da ba wa matasa kwarin guiwa. Hakan kuwa zai tabbatar da habaka da cigaban rayuwar mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel