‘Dan Zakzaky ya bayyana damuwarsa da halin da iyayensa za su shiga a kurkukun Kaduna

‘Dan Zakzaky ya bayyana damuwarsa da halin da iyayensa za su shiga a kurkukun Kaduna

Yaron shugaban yan Shia, Mohammed Zakzaky ya bayyana damuwarsa bisa halin da iyayensa za su shiga idan har aka mayar dasu gidan kurkukun jahar Kaduna duba da rashin lafiyar da suke fama da shi a yanzu haka.

Jaridar Sahara ta ruwaito a ranar Juma’ar data gabata ne wata babbar kotun Kaduna ta bada umarnin dauke da Zakzaky daga babban ofishin hukumar DSS dake babban birnin tarayya Abuja tare da mayar da shi kurkukun Kaduna domin lauyoyinsa su samu saukin ganawa da shi a duk lokacin da bukatar hakan ta kama.

KU KARANTA: Rikicin zabo magajin Buhari: An sa zare tsakanin gwamnonin APC da shugaban APC

Sai dai Mohammed yace dauke iyayensa daga Abuja zuwa Kaduna zai zamto babban kalubale ga lafiyar iyayensa, duba da lalacewar dake tattare da gidajen yarin Najeriya, wanda yace a maimakon mara lafiya ya samu sauki sai dai ma su kara masa cuta.

“Sanin kowa ne halin da kurkuku suke ciki sai dai su kara ma mutum rashin lafiya, balle kuma wadanda suna cikin mawuyacin hali, don haka nake bayyana damuwana da yadda gwamnatin Najeriya ke nuna halin ko in kula da mahaifina Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da babarmu Zeenah.

“Mahaifina baya gani a sakamakon harbinsa da aka yi a lokacin da aka kai mana hari a shekarar 2015, haka zalika mahaifiyata bata da lafiya, da kyar take tafiya, kuma tana dauke da harsashi a kusa da kashin ta na baya.” Inji shi.

Idan za’a tuna tun a shekarar 2015 aka kama Zakzaky da matarsa inda gwamnatin jahar Kaduna take tuhumarsa da laifukan da suka danganci kisan kai, gangami ba bisa kaida ba, tayar da hankulan jama’a da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel