Da duminsa: Kotu ta dakatar da Ganduje daga kafa majalisar Sarakuna da nada mambobinta

Da duminsa: Kotu ta dakatar da Ganduje daga kafa majalisar Sarakuna da nada mambobinta

Wata babbar kotun jihar Kano, Jastis A. T Badamosi, ta dakatar da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, daga kafa majalisar sarakuna da nada mambobinta.

A ranar Litinin ne gwamna Ganduje ya nada sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban sabuwar majalisar sarakunan Kano da ya kafa bayan kirkirar sabuwar dokar masarautu.

Kotun ta zartar da hukuncin ne a yayin zamanta na ranar Talata.

A wani martani da ya mayar ga kungiyar dattijan jihar Kano da suka nemi ya janye dokar kirkirar sabbin masarautu, Ganduje ya bayyana cewa kungiyar ba zata iya canja shawarar da ya yanke na kirkirar sabbin masarautu a jihar ba.

Da duminsa: Kotu ta dakatar da Ganduje daga kafa majalisar Sarakuna da nada mambobinta

Ganduje da sabon sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Source: Twitter

A cewar gwamnan, babu abin da zai sauya dokar kirkirar sabbin masarautun tunda dai ta bi dukkan wani matakin doka kafin a tabbatar da ita.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen 'yan majalisar Sarkin Karaye da ya rantsar

A ranar Litinin ne dattawan jihar Kano a karkashin kungiyar hadin kan Kano, ta yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar ganduje da ya janye dokar kirkirar karin masarautu a jihar.

A takardar da aka fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Tofa, tare da wasu dattawa goma kuma suka mika ga manema labarai, dattawan sun nuna fushinsu a kan yunkurin gurbata tarihin masarautar na sama da shekaru 1000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel