Tababa a kan sabbin masarautu: Ganduje ya mayar wa da dattawan Kano martani

Tababa a kan sabbin masarautu: Ganduje ya mayar wa da dattawan Kano martani

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani ga kungiyar dattijan jihar a kan kira da suka yi masa na ya janye dokar kirkirar sabbin masarautu hudu masu sarakunan yanka a Kano.

Ganduje ya bayyana cewa kungiyar ba zata iya canja shawarar da ya yanke na kirkirar sabbin masarautu a jihar ba.

A cewar gwamnan, babu abin da zai sauya dokar kirkirar sabbin masarautun tunda dai ta bi dukkan wani matakin doka kafin a tabbatar da ita.

A ranar Litinin ne dattawan jihar Kano a karkashin kungiyar hadin kan Kano, ta yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar ganduje da ya janye dokar kirkirar karin masarautu a jihar.

A takardar da aka fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Tofa, tare da wasu dattawa goma kuma suka mika ga manema labarai, dattawan sun nuna fushinsu a kan yunkurin gurbata tarihin masarautar na sama da shekaru 1000.

Tababa a kan sabbin masarautu: Ganduje ya mayar wa da dattawan Kano martani

Bashir Tofa
Source: Twitter

Idan zamu tuna, majalisar jihar Kano ta amince da bukatar karin kirkirar sabbin masarautu hudu a jihar a ranar 5 ga watan Disamba. A ranar Alhamis din ne kuma Abdullahi Ganduje yasa hannu a sabuwar dokar.

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi ya aike wa gwamnatin tarayya sako

Duk da wannan ne karo na biyu da Gwamnan ya mika wannan bukatar ga majalisar, an fara sa hannu a kanta ne a watan Mayu 2019. Amma babbar kotun jihar Kano din ta shafe dokar a ranar 21 ga watan Nuwamba karkashin jagorancin mai shari'a Jastis Usman Na'Abba.

Takardar ta ce, "Kungiyar hadin kan jihar Kano ba kungiyar siyasa bace ko kuma mai goyon bayan wani mutum ba. Kungiya ce da ke bin doka kuma masu mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban jihar Kano.

"A don haka ne, muke nuna damuwarmu a kan yadda Gwamna Ganduje ya jajirce don tarwatsa masarautar jihar Kano. Wannan kuma kokari ne wanda kakanninmu suka yi na karni aru-aru," in ji takardar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel