Abubuwan da su ka yi sanadiyyar maye gurbin Tunde Fowler a FIRS da M. M Nami

Abubuwan da su ka yi sanadiyyar maye gurbin Tunde Fowler a FIRS da M. M Nami

Tun daga lokacin da fadar shugaban kasa ta aika wata takarda ga shugaban hukumar FIRS na wancan sa’ili, masu lura da al’umura su ka fahimci cewa aikin Tunde Fowler ya zo karshe.

A Ranar 9 ga Watan Disamban 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya nada Muhammad Nami a kan kujerar hukumar FIRS, tare da la’kari da tantancewarsa a gaban majalisar dattawan kasar.

Jaridar Pulse ta kawo dalilai da ake zargin cewa su su ka sa Fowler bai samu karin wa’adi ba.

1. Karancin kudin shiga

Duk da irin kokarin da Babatunde Fowler ya yi a ofis, ana ganin cewa hukumar FIRS ta na gaza cika alkawarin da ta dauka duk shekara na tatsar kudin shiga. Fadar shugaban kasar ta jawo hankalin Tunde Fowler a game da wannan tun watanni hudu da su ka wuce, ya kuma kare kansa.

2. Zargin rashin gaskiya

Ana zargin hukumar FIRS a karkashin Babatunde Fowler da facaka da dukiyar kasa da rashin binciken kudin da ke shiga ya na fita. Har ila yau jaridar ta ce akwai zargin bada kwangiloli ga ‘Yan gaban goshi a hukumar. Ana zargin shi kan sa Fowler da samun Digirin bogi a kasar waje.

KU KARANTA: An aikawa ‘Yan Majalisa takarda kan nadin sabon Shugaban FIRS

3. Badakalar kudi da daukar aiki

Akwai zargin da ke kan wuyan tsohon shugaban hukumar na cewa ya dauki sama da mutane 300 aiki a boye. Bayan haka akwai manyan jami’an FIRS da ake zargi da laifin wawurar kudin harajin da aka tara, wannan ya sa EFCC ta bi ta kan irinsu Abumere Joseph Osagie a ‘yan shekarun baya.

4. Kwadayin a kara ba shi dama

Pulse ta na ganin roko kara-ra na sake nada shi a matsayin shugaban hukumar tattara haraji a karo na biyu, ya na cikin abubuwan da su ka sa fadar shugaban kasa ta nemi sabon shugaba a wannan karo. Daga baya Babatunde Fowler ya nuna cewa dama can ba dole ba ne ya zarce a ofis.

5. Yaron Tinubu

A ra’ayin wasu, sallamar Fowler bayan cikar wa’adinsa na fari ya na da burbushin siyasa. Yin hakan ya na da tasiri wajen taba siyasar Kudu maso Yammacin kasar, musamman yadda ake ganin akwai hannun Bola Tinubu da Mai girma Yemi Osinbajo wajen nadin sa a shekarar 2015.

6. Shekaru sun ja

A shekara fiye da 60 a Duniya, Babatunde Fowler ya kai wani mataki da iya cewa ya fara tsufa. Tsakanin 2005 zuwa 2013, kwararren Ma’aikacin ya ci lokacinsa a hukumar tattara harajin Legas, inda ya shafe shekaru 8 a kan kujera. Kara masa wani wa’adi zai sa ya bar ofis ya na shekara 68.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel