Yanzu-yanzu: Buhari ya sake sallaman wani yaron Tinubu, ya nada Adamu sabon shugaban AMCON

Yanzu-yanzu: Buhari ya sake sallaman wani yaron Tinubu, ya nada Adamu sabon shugaban AMCON

Cikin sa'o'i 24, shugaba Muhammadu Buhari ya sallami yaran Tinubu guda biyu daga manyan kujerun da suke rike da shi.

Kamar yadda ya bayyana da ranan nan, shugaba Buhari ya bayyana Mista Edward Adamu matsayin sabon shugaban hukumar lura da dukiyoyi a Najeriya wato AMCON.

Wannan na kunshe cikin wasikar da ya aikawa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, kuma ya karantaa zauren majalisa ranar Talata, 10 ga Disamba, 2019.

Nadin Edward Adamu ya kawo karshen mulkin Dakta Muiz Banire wanda yake rike da kujerar tun Yulin 2018.

Hakazalika, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Muhammad M. Nami a matsayin shugaban hukumar kudin shiga ta tarayya, FIRS.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Nami zai maye gurbin Tunde Fowler, wanda wa'adin mulkinsa ya kare a ranar Litinin da ta gabata.

Sabon shugaban hukumar, kwararre ne a bangaren haraji kuma ya kammala karatunsa ne a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

A ranar da aka ya nada sabon shugaba, Babatunde Fowler ya nemi shugaba Muhammadu Buhari ya kara masa wani sabon wa’adin shekaru hudu a hukumar FIRS mai alhakin tatattara haraji a Najeriya, saboda irin ayyukan a zo a ganin da yayi.

Tsohon shugaban hukumar ta FIRS ya aikawa gwamnatin shugaba Buhari takarda ya na mai neman a kuma ba shi wata damar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel