Ka yi wa ‘Yan kasa bayani a kan N6bn, da $91m na NDDC – Majalisa ga Akpabio

Ka yi wa ‘Yan kasa bayani a kan N6bn, da $91m na NDDC – Majalisa ga Akpabio

Sa-in-sar da ake samu tsakanin ‘Yan majalisar tarayya da Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio ya kai wani mataki inda ake cigaba da zargin Ma’aikatar da yin ba daidai ba.

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa ana ta maidawa juna kalaman zargi tsakanin Sanatocin kasar da Ministan game da bata lokacin da ake samu wajen kafa shugabannin hukumar NDDC.

Yayin da majalisa ta ke magana a kan zargin da ake yi mata na karbar Naira biliyan 1 a madadin hukumar NDDC, majalisar tarayyar ta bukaci a fito da hujjojin da za su gamsar da wannan zargin.

‘Yan majalisar dattawan sun yi wannan bayani ne ta bakin shugaban kwamitin da ke kula da harkar NDDC, Sanata Peter Nwaoboshi. Sanatan ya bukaci a fito da takardu da ke gaskata zargin.

KU KARANTA: Buhari zai tafi kasar waje tare da wasu Ministoci da Gwamnoni

Ka yi wa ‘Yan kasa bayani a kan N6bn, $91m na NDDC – Majalisa ga Akpabio

An daurawa Akpabio laifin bata lokaci wajen kafa shugabannin NDDC
Source: UGC

Nwaoboshi ya fitar da wannan jawabi ne ta hannun Mai taimaka masa kan harkokin majalisa, ya na zargin Minista da jawo bata lokacin da aka samu wajen nada sababbin shugabannin NDDC.

Luka Igbonoba, a madadin Sanatan ya jefawa Sanata Godswill Akpabio kalubalen yi wa mutane bayanin inda Dala miliyan 91 da Naira biliyan 6 da ke cikin asusun hukumar NDDC su ka shige.

A cewar Hadimin Sanatan, wadannan makudan kudi su na karkashin ma’aikatar harkokin Neja-Deltan. The Guardian ta fito da wannan rahoto ne a Ranar Litinin. 9 ga Watan Disamban, 2019.

A bangare guda, Darektan NDDC na kasa, Gbene Nunieh, ya bayyana cewa yanzu an dakatar da karbar wannan kudi da aka saba har Naira biliyan 1 duk wata daga hannun kamfanonin mai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel