Buhari: Mataimakin Gwamnan CBN Adamu zai jagoranci AMCON, Nami zai rike FIRS

Buhari: Mataimakin Gwamnan CBN Adamu zai jagoranci AMCON, Nami zai rike FIRS

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da wasika gaban majalisar dattawa, ya na rokon a tabbatar masa da Muhammad Mamman Nami a matsayin sabon shugaban hukumar FIRS.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasar ya zabi Muhammad Nami a Ranar Litinin dinnan a matsayin wanda zai gaji Babatunde Fowler a hukumar FIRS mai tattara haraji a Najeriya.

Bayan nadin sabon shugaban FIRS, Muhammadu Buhari, ya bukaci ‘yan majalisar dattawan kasar su tantance Edward Lametek Adamu a matsayin wanda zai jagoranci hukumar AMCON.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ne ya karanto takardar Mai girma shugaban kasar a zaman da ake yi a yau dinnan, Talata 10 ga Watan Disamban 2019.

Dr. Ahmad Lawan ya karanto wasikun shugaban kasar ne dazu kamar yadda mu ka samu labari daga shafin majalisar dattawan kasar jim kadan bayan ‘yan majalisar sun dawo bakin aiki.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban FIRS ya godewa damar da Buhari ya ba shi

Kamar yadda rahotanni su ke zuwa mana, a cikin wasikar da aka aiko daga fadar shugaban kasar, akwai sunayen wadanda shugaba Buhari ya ke so su rika kula da hukumar FIRS ta kasar.

Mista Nami ya fito ne daga tsakiyar Arewacin Najeriya, kuma kwararre ne a kan sha’anin haraji. Shi ne ake sa rai zai karbi aikin da Tunde Fowler, wanda ya fito daga Kudancin kasar ya bari.

A sabuwar dokar AMCON, za a samu wani cikin mataimakan gwamnonin babban bankin CBN da zai rika sa idanu a aikin hukumar. Edward Adamu ya na cikin mataimakan gwamnonin CBN.

Sauran masu taimakawa Godwin Emefiele a babban bankin na CBN a yanzu sun hada da: Dr. Okwu Joseph Nnanna, Misis Aishah N. Ahmad, sai kuma Mista Folashodun Adebisi Shonubi

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel