Rikicin zabo magajin Buhari: An sa zare tsakanin gwamnonin APC da shugaban APC

Rikicin zabo magajin Buhari: An sa zare tsakanin gwamnonin APC da shugaban APC

Rikicin gida ya kunno kai a tsakar gidar jam’iyyar APC, kuma yana kara ruruwa sakamakon zare da aka sanya tsakanin shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole da gwamnonin jam’iyyar APC a kan wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Jaridar Punch ta binciko duk da zaman tattaunawa da aka yi tsakanin Buhari da gwamnonin APC a ranar Alhamis, da kuma ganawar da yayi da shuwagabannin jamiyyar APC na jahohi 36 a ranar Juma’a, har yanzu tsuguni bata kare ba, sakamakon wasu gwamnoni sun dage lallai sai Oshiomole ya tafi.

KU KARANTA: Majalisa ta yi zargin almundahana a yadda aka sayar da wutar lantarkin Najeriya ga yan kasuwa

Rikicin zabo magajin Buhari: An sa zare tsakanin gwamnonin APC da shugaban APC

Rikicin zabo magajin Buhari: An sa zare tsakanin gwamnonin APC da shugaban APC
Source: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ba wani abu bane ya kawo wannan rikici illa burin wasu gwamnonin APC na zakulo wanda zai gaji shugaban kasa a zaben 2023 daga cikinsu, don haka suke kokarin sutale Oshiomole daga kujerarsa domin sun fahimci zai iya kawo musu tarnaki.

A yayin ganawarsu da shugaba Buhari, shugaban kungiyar shuwagabannin APC a matakin jaha, kuma shugaban APC a Zamfara, Ali Bukar ya nemi Buhari ya ja kunnen wasu gwamnoni wanda yace suna shirin jefa jam’iyyar cikin rudani.

“Mun damu kwarai game da yadda wasu gwamnoni ke kokarin yin zagon kasa ga shugaban jam’iyyarmu ta kasa, Adams Oshiomole ta hanyar tsige duk kuwa da kokarin da yake yi.

"Abin haushin ma shi ne kowa ya sani suna yin wannan ne ba wai don bai yi kokari ba, suna yi ne kawai don bukatarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 duk kuwa da cewa shugaban kasa bai wuce yan watanni a zangonsa na biyu ba.” Inji shi.

Wata majiya daga shugabancin APC na kasa ta tabbatar ma majiyarmu cewa gwamnonin APC ne suka janyo wannan rikici ba don komai ba sai don biyan bukatansu, inda yace musamman wadanda zasu kammala wa’adin mulkinsu a 2023.

“Burinsu su nada magada a jahohinsu, sa’annan kuma su zakulo wanda zai gaji Buhari daga cikinsu, don haka suke ganin idan har basu kama jam’iyyar a kowanne mataki ba ba zasu taba samun nasara ba. Kuma sun san Oshiomole nada taurin kai, don haka suke son maid an gwabi gwabi da zai amince da bukatunsu.” Inji shi.

A yanzu dai yan Najeriya za su zura idanu don ganin yadda za ta kaya a tsakanin wadannan giwayen siyasa guda biyu don sanin wa gari zai waya?

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel