Kadarar Jide Omokore ta koma hannun hukumar AMCON – Inji Kotu

Kadarar Jide Omokore ta koma hannun hukumar AMCON – Inji Kotu

Wani babban kotun tarayya tarayya ya yanke hukunci cewa hukumar AMCON mai kula da kadarorin Najeriya ta karbe kamfanin man nan na “Cedar Oil & Gas Exploration & Production.”

Bashin Naira biliyan 29 da ake bin wannan kamfanin mai ne ya sa Alkalin kotun da ke Legas, mai suna C.J. Aneke ya bada umarnin kamfanin ya koma karkashin kulawar gwamnatin tarayya.

A halin yanzu hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta taso keyar Jide Omokore a gaba bisa zargin wawurar dukiyar kasa. Omokore ya na cikin na-hannun daman Diezani Alison-Madueke.

Ita kan ta Madam Diezani Alison-Madueke, ta na karkashin binciken hukumomin Najeriya da kasar waje. Mista Jide Omokore shi ne wanda ya mallaki kamfanin Atlantic Energy Limited.

KU KARANTA: Mompha ya sha iskar wajen gidan yari bayan biyan beli

Kadarar Jide Omokore ta koma hannun hukumar AMCON – Inji Kotu

Alkalin Kotun Legas ya ce AMCON ta karbe kamfanin su Jide Omokore
Source: UGC

Alkali mai shari’a C.J. Aneke ya amince da rokon da hukumar AMCON ta ke yi na mika mata kadarar Jide Omokore saboda taurin-kai da ya yi wajen biyan bashin da ya karba daga bankuna.

Mai magana a madadin hukumar ta AMCON na kasa, Jude Nwauzor, ya tabbatar da cewa sun bi umarnin kotu, don haka yanzu wannan kamfani da abin da su ka mallaka ya koma hannun su.

Daga cikin kadarorin da hukumar ta karbe akwai wani gida da ke kan layin Gerrard a Unguwar Ikoyi, a jihar Legas. Haka zalika hukumar ta karbe wani katafaren gida da ke Maitama a Abuja.

Alkali ya yanke wannan hukunci ne bayan Darektocin wannan kamfani; Olajide Omokore, Isiaka Mohammed, Joseph Bazuaye, da Silas Ode, sun ki maida kudin da su ka ara a hannun bankuna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel