Jami'an Kwastam sun damke katon 640 na kwayoyin karfin maza mai suna "AK47"

Jami'an Kwastam sun damke katon 640 na kwayoyin karfin maza mai suna "AK47"

Hukumar hana fasa kwabri wato Kwastam ta yi arangama da katon-katon na kwayoyin karfin maza (kwayoyin karawa maza kuzari wajen jima'i) guda 640 kimanin kudi N914.8 million.

A jawabin da kakakin hukumar Kwastam, Magaji Mailafiya, ya saki, ya bayyana cewa an dakile kwayar mai suna "A kashe mata" ko "AK47" ne a hanyar Illela-Kwara ranar 24 ga Nuwamba, 2019.

Hakazalika, hukumar a ranar 25 ga Nuwamba ta damke wasu motoci kirar Toyota Carina II guda uku masu lambobi AG 462 WSN, ER 415 ABJ da AZ 509 SRZ jibge da galolin man gyada 132, katon 85 na batir da buhuhuna 86 na MaginAjino Moto ko Vedan a hanyar Achida/Goronyo.

Bugu da kari, a ranar 20 ga Nuwamba, an damke adduna 800 a Illela, yayinda akayi kokarin shigo da su Najeriya.

Hukumar ta yi kira ga al'umma su rungumi hallatun kasuwanci kuma su daina kokarin fasa kwabrin haramtattun kayayyaki.

Ta lashi takobin cewa ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen dakile duk masu irin halin fasa kwabri a yankin.

Mun kawo muku rahoton cewa Jami'an hukumar Kwastam sun damke wani matashi da ya kanannade shinkafa a jikinsa domin shigo da su Najeriya.

A bidiyon da muka samu a manhajar Facebook, an ga jami'in kwastam yana yanke selotep din da akayi amfani da shi wajen daure shinkafar a sassan jikinshi daban-daban. An daura wasu a kirginsa, wasu a kafansa.

Ana iya jin murya a cikin bidiyon inda jami'in ke cewa mai laifin dake kokarin boye fuskarsa ya daga kai ya fuskanci kamara.

Daga baya daya daga cikin jami'an ya kawo buhu domin juya shinkafar gwamnatin ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel