Harin ta’addanci: Wani dan bindiga ya halaka mutane 6 a cikin Asibitin Czech Republic

Harin ta’addanci: Wani dan bindiga ya halaka mutane 6 a cikin Asibitin Czech Republic

Wani dan bindiga dadi ya kaddamar da harin mai kan uwa da wabi a wani asibitin kasar Czech Republic, inda a dalilin haka ya halaka akalla mutane shida, tare da jikkata wasu da dama, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Talata a wani asibiti dake birnin Ostrava, cikin yankin Arewa maso gabashin kasar Czech Republic. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa dan bindigan ya ranta ana kare.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta yi rabon kayan abinci ga zawarawa da marayu a jahar Adamawa

“An kwashe duk jama’an dake cikin asibitin, amma har yanzu Yansanda suna farautar mutumin daya aikata laifin.” Inji Yansanda.

A wani labarin kuma, wani babban kwamandan yaki na rundunar Sojan kasa ta Najeriya ya gamu da ajalinsa yayin da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka dasa wani bom a kusa da motarsa wanda ya tashi da shi.

Wannan lamari ya faru ne a garin Marten a jahar Borno kamar yadda wasu majiyoyi na karkashin kasa daga rundunar Sojan suka tabbatar, inda suka ce jami’in Sojan shi ne kwamandan bataliya ta 153 dake Marte.

Majiyoyin sun kara da cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, 7 ga watan Disamba yayin da kwamandan yake jagorantar Sojojinsa zuwa aikin sintiri, a daidai wannan lokaci ne bom din ya tashi da motar kwamandan.

Wasu majiyoyi na daban sun tabbatar da mutuwar kwamandan, amma sun ce babu tabbacin ko shi kadai ne ya mutu, ko kuma akwai wasu Sojoji na daban basu mutu ba, sai dai majiyarmu ta ki bayyana sunan mamacin sakamakon babu tabbacin ko iyalansa suna da masaniya ko kuwa a’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel