Majalisa ta yi zargin almundahana a yadda aka sayar da wutar lantarkin Najeriya ga yan kasuwa

Majalisa ta yi zargin almundahana a yadda aka sayar da wutar lantarkin Najeriya ga yan kasuwa

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa akwai almundahana a yadda tsohuwar gwamnatin shugaba Jonathan ta cefanar da kamfanin wutar lantarkin Najeriya a shekarar 2013.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Lawan ya bayyana haka ne yayin da yake bude taron tattauna a kan matsalar wutar lantarki wanda kwamitin wutar wutar lantarki na majalisar dattawa ta shirya, inda ya yi kira ga gwamnatin Buhari ta kaddamar da dokar ta baci a sha’anin wuta a Najeriya.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta yi rabon kayan abinci ga zawarawa da marayu a jahar Adamawa

“A wajena, idan har akwai wani fanni da ya fi kowanne amfani amma kuma yake fuskantar kalubale babu kamar sha’anin wutar lantarki a Najeriya, ina ganin akwai bukatar kaddamar da dokar ta baci a wutar lantarki a Najeriya.

“Gaskiyar magana ita ce mun san babban matsalar, abin da ya kamata kawai shi ne shuwagabannin siyasa su dauki matakin da suka san shi yafi dacewa game da wannan matsala.

"Tun daga gyaran fuskar da aka yi ma dokar wutar lantarki a shekarar 2005 zuwa sayar da kamfanonin dake samar da wuta da wadanda ke raba wutar duk mun san cike suke da almundahana. Idan muka yi biris da matsalar, zamu cigaba da tattauna matsalar wuta har shekaru 10 masu zuwa.” Inji shi.

Sai dai kammala jawabin shugaban majalisar dattawa ke da wuya, sai wakiliyar kamfanin Energy Market and Rate consultant, Rahila Thomas tace idan har gwamnati na so a samu wuta isashshe a Najeriya, sai ta antaya kimanin kudi naira triliyan 1.23 ga kamfanonin samar da wutar lantarki da masu rarraba wutar.

A wani labarin kuma, hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta bayyana cewa a yanzu haka tana gudanar da bincike a kan tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Abdulaziz Yari bisa wasu kudin kwangila naira biliyan 900 da suka yi batan dabo a gwamnatinsa.

Shugaban hukumar, reshen jahar Sakkwato, Abdullahi Lawal ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba yayin zagayen wayar da kai don tunawa da ranar yaki da rashawa ta duniya a tashar motar Hajia Halima dake Sakkwato.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel