Ba mu tare da batun biyan kudin lasisi da shaidar aure a coci - Kungiyar PFN

Ba mu tare da batun biyan kudin lasisi da shaidar aure a coci - Kungiyar PFN

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa wata kungiyar PFN ta Darikar Kiristocin Najeriya, ta nuna rashin goyon bayanta ga sabuwar dokar aure da gwamnatin tarayyar kasar ta kawo.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za a rika biyan N30, 000 a matsayin kudin lasisi idan aka daura aure a coci. Bayan haka kuma za a rika karbar N21, 000 domin samun shaidar satifiket.

Kungiyar PFN ta bakin shugabanta na kasa, Felix Omobude, ta yi tir da wannan mataki da Ma’aikatar cikin gida ta dauka da cewa ana yunkurin maida auren zobe tamkar wani kasuwanci.

Dr. Felix Omobude a wani jawabi da ya fitar a Garin Benin, ya shaidawa ‘Yan jarida cewa wannan doka da gwamnatin tarayya ta kakaba a kan cocin da ke kasar ya sabawa shari’ar addinin kirista.

KU KARANTA: An sace Fastocin a kan hanyar zuwa daurin aure a Kudancin Najeriya

Ba mu tare da batun biyan kudin lasisi da shaidar aure a coci - Kungiyar PFN

PFN ta ce Kiristoci ake hari idan aka lafta kudi a wajen aure
Source: Facebook

Jawabin Felix Omobude ya ce: “A iyaka sani na, ana harin coci ne da wannan sabuwar doka, domin ba a biyan wani kudin satifiket idan an daura auren musulunci ko kuma na gargajiya.”

Shugaban kungiyar addinin ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta janye wannan tsari maras farin jini da aka shigowa Kiristocin Najeriya da shi. Gwamnatin kasar ba ta maida martani ba tukuna.

Dr. Omobude ya kara da cewa: “Idan Ma’aikatar harkokin cikin gida su na da matukar bukatar kudi, ta nemi hanyar da za ta samu, amma ba ta hanyar daura nauyi a kan Kiristoci da coci ba."

Kungiyar addinin ta karkare jawabin ta da cewa: “PFN za ta bi duk hanyar da ta halatta wajen ganin ta sa gwamnatin tarayya ta janye matakin da ta dauka a kan wannan dokar shaidar aure.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel