An yankewa Likitan da ya kashe mutane 15 a Adamawa hukuncin shekaru 54 a gidan yari

An yankewa Likitan da ya kashe mutane 15 a Adamawa hukuncin shekaru 54 a gidan yari

Wata babbar kotun garin Yola ta yankewa Likitan bogi, Ibrahim Mustapha, hukuncin shekaru 54 a gidan yarin jihar Adamawa.

Alkali mai shari'a, Nathan Musa, yayinda yake yanke hukuncin jiya yace likitin bogi, Ibrahim Mustapha, ya cancanci ukuba mai tsanani saboda karyan cewa yayi karatun likitanci alhalin kwalin sakandare yake da shi.

Alkalin yace: "Allah kadai ya san irin lalatan da kayi a matsayin likitan bogi."

Ibrahim ya kwashe shekaru da dama yana aiki matsayin Likita a karkashin gwamnatin jihar Adamawa da kwalin digirin bogi.

Ya zama babban likita a asibitin Cottage dake karamar hukumar Fufore, amma dubunsa ya cika a watan Yunin 2019 da hukumar DSS ta damkeshi.

DUBA NAN: Mompha ya cika sharrudan beli, EFCC ta sakeshi (Bidiyo)

Diraktar DSS na jihar, Bola Olori, ta bayyanawa manema labarai cewa kwalin da Ibrahim Mustapha ya mallaka shine NBTE, wanda yake kwatankwacin kwalin kare karatun sakandare.

Daga baya, Ibrahim ya laburta cewa lallai kwalayen karatun Likitan bogi yake amfani da su amma ya musanta zargin cewa ya kashe mutane.

Yace: "Lallai hakane, takardun bogi ne kamar da shugabar DSS ta fada."

"Na gudanar da ayyukan tiyata manya da kanana sama da 500, har da masu juna biyu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel