FIRS: Fowler ya roki Shugaban kasa ya kara masa wa’adi kafin a nada Nami

FIRS: Fowler ya roki Shugaban kasa ya kara masa wa’adi kafin a nada Nami

Babatunde Fowler ya nemi shugaba Muhammadu Buhari ya kara masa wani sabon wa’adin shekaru hudu a hukumar FIRS mai alhakin tatattara haraji a Najeriya, amma bai samu ba.

Tsohon shugaban hukumar ta FIRS ya aikawa gwamnatin shugaba Buhari takarda ya na mai neman a kuma ba shi wata damar. Fowler ya aika wasikarsa ne ga Sakataren gwamnatin tarayya.

A Ranar da Fowler ya aika wannan takarda, Buhari ya sanar da nadin Muhammad Nami a matsayin wanda zai gajesa a hukumar. An yi wannan ne a Ranar 9 ga Watan Disamba, 2019.

Mista Fowler ya fadawa SGF, Boss Mustapha cewa za a cigaba da ganin kakarin kokarin da ya saba idan aka sake ba shi damar sake jan ragamar hukumar FIRS ta kasar, a wani danyen karo.

Dokar FIRS ta bada dama ga shugaban hukumar ya zarce zuwa karo na biyu. Kowane wa’adi ya na da tsawon shekaru hudu. Tunde Fowler ya dare kan wannan kujera ne a farkon Disamban 2015.

KU KARANTA: Abin da Fowler ya fada bayan Buhari ya maye gurbinsa da Nami

Kamar yadda mu ka samu labari, a cikin wasikar da ya aikawa SGF, tsohon shugaban na FIRS ya kunsa takardun irin nasarori da cigaban da hukumar ta samu a cikin shekaru hudun da ya yi.

Mai barin gadon ya ce: “Na rubuto wannan domin in sanar da Sakataren gwamnatin tarayya cewa wa’adi na a matsayin shugaban hukumar FIRS ya kare yau, 9 ga Watan Disamban 2019.”

“A dalilin wannan ne, na ke gabatar da kai na domin a kara mani wa’adi na biyu. Wannan ya na cikin dokar FIRS ta 2007, idan aka bani dama, zan dada a kan kokarin da mu ka yi a shekaru 4.”

Wasikar ta kare da cewa: “Za a samu bayanai kunshe da nasarorin da aka samu a wa’adin farko da na yi a ofis.” Yanzu dai Fowler ya bar ofis, ya mikawa Abiodun Aina karaga kafin zuwa Nami.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel