Mompha ya cika sharrudan beli, EFCC ta sakeshi (Bidiyo)

Mompha ya cika sharrudan beli, EFCC ta sakeshi (Bidiyo)

- Shahrarren wanda ake zargi da damfara, Ismaila Mustapha wanda akafi sani da Mompha ya samu yanci bayan biyan belin N100m

- Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta damkeshi ne ranar 19 ga Oktoba kan zargin damfarar N33bn

- Bidiyoyin lokacin da Mompha ya fito sun bayyana a kafafen Soshiyal Midiya

Shahrarren matashin nan mai bayyana arzikinsa a kafafen soshiyal, Ismaila Mustapha, ya fito daga kurkukun EFCC bayan cika sharrudan belinsa.

Babban kotun tarayya dake Legas ta baiwa shahararren matashin nan mai alfahari da daloli kuma ake zargi da damfara, Ismaila Mustapha, beli.

Kotun ta baiwa matashin da akafi sani da suna 'Mompha' belin N100m.

An gurfanar da Mompha ne kan zargin damfarar N33billion.

Mompha ya cika sharrudan beli, EFCC ta sakeshi (Bidiyo)

Mompha ya cika sharrudan beli, EFCC ta sakeshi (Bidiyo)
Source: Facebook

Magu ya bayyana cewa Ismail Mustapha ya saci makudan kudade da suka kai naira biliyan 14 ta kamfaninsa mai suna Imalob Global Investment Limited, sa’annan yana amfani da asusun ajiyan kudi na banki guda 51.

A ranar 19 ga watan Oktoba, 2019, jami'an EFCC suka damke Ismail Mompha a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja yayinda yake kokarin shilawa Dubai.

Magu yace yace Mompha ya mallaki kadarori da dama a Dubai, baya ga agoguna guda 5 da aka kwace daga hannunsa da suka kai naira miliyan 60.

Kalli bidiyon:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel