Aisha Buhari ta yi rabon kayan abinci ga zawarawa da marayu a jahar Adamawa

Aisha Buhari ta yi rabon kayan abinci ga zawarawa da marayu a jahar Adamawa

Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, ta yi rabon kayan abinci da kudi ga marayu da gajiyayyu a jahar Adamawa, wanda suka tasan ma miliyoyin nairori, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Aisha Buhari wanda ta samu wakilcin Hajiya Fatima Rafindadi ta yi rabon kayan ne a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba a garin Yola, inda ta shaida cewa sun yi rabon ne daga cikin ayyukan gidauniyar Aisha Buhari ta ‘Future Assured’.

KU KARANTA: Muhimman batutuwa 11 game da Muhammad Nami, sabon shugaban hukumar FIRS

Aisha tace babbar manufar rabon kayayyakin shi ne bayar da gudunmuwa ga ayyukan gwamnatin tarayya na inganta rayuwar yan Najeriya, musamman wadanda suka fito daga yankunan karkara. Kayan sun hada da buhunan shinkafa, doya, man girki da atampopi.

“A yau kungiyoyi 20 sun samu tallafin kayan abinci da kudi, gidauniyar Future Assure ce ta dauki wannan aikin, kuma ta yi haka ne domin taimakawa wajen inganta rayuwar gajiyayyu da marasa karfi a duk fadin kasar nan.” Inji ta.

A jawabinta, uwargidar gwamnan jahar Adamawa, Hajiya Lami Fintiri, wanda ta samu wakilcin babbar sakatariya a ma’aikatan kula da sha’anin mata ta jahar Adamawa, Justina Patrick ta bayyana godiyarta ga uwargidar shugaban kasa game da wannan aikin alheri.

Lami ta bayyana cewa tallafin zai amfani wadanda suka amfana, don haka ta yi kira a garesu dasu tabbata sun yi amfani da kayan da suka samu ta hanyar daya kamata. Su ma wasu da suka amfana da aikin alherin sun yi fatan Allah Ya saka ma Aisha da alheri.

Daga cikin kungiyoyin da suka samu wannan tallafi akwai kungiyoyin mata da suka rasa mazajensu, gidajen marayu, hukumar sauya halayya ta Najeriya, kungiyar mata musulmai, kungiyar kiristoci da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel