EFCC ta fara binciken Abdulaziz Yari a kan satar naira biliyan 900 kudin kwangila

EFCC ta fara binciken Abdulaziz Yari a kan satar naira biliyan 900 kudin kwangila

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta bayyana cewa a yanzu haka tana gudanar da bincike a kan tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Abdulaziz Yari bisa wasu kudin kwangila naira biliyan 900 da suka yi batan dabo a gwamnatinsa.

Shugaban hukumar, reshen jahar Sakkwato, Abdullahi Lawal ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba yayin zagayen wayar da kai don tunawa da ranar yaki da rashawa ta duniya a tashar motar Hajia Halima dake Sakkwato.

KU KARANTA: Muhimman batutuwa 11 game da Muhammad Nami, sabon shugaban hukumar FIRS

Jaridar ThisDay ta ruwaito shugaban hukumar yana cewa wadannan makudan kudade da ake tuhumar Yari a kansu an fitar dasu ne da nufin gudanar da kwangiloli daban daban, amma kuma ba’a gudanar da kwangilolin ba, kuma babu kudin.

A hannu guda kuma, Lawal yace tun watan Oktoban shekarar 2018 da aka bude ofishin hukumar EFCC a Sakkwato sun samu kararraki guda 236, inda suke binciken guda 151, sun gabatar da guda 20 a gaban kotu, yayin da sun samu nasara a guda 4.

Ya kara da cewa sun kwato zambar kudi naira miliyan 910, sun kai naira miliyan 125 zuwa babban bankin Najeriya domin ajiya, sa’annan sun kwato CFA 36,000, manyan motocin alfarma guda 4 da keke napep 53.

Lawal ya bayyana cewa a yanzu haka suna binciken wani dan kwangila a jahar Zamfara da aka bashi aikin gina famfon tuka tuka guda 287 a kan kudi naira biliyan 200 tun a shekarar 2013, amma bai yi aikin ba, haka zalika suna binciken wani Sanata daya ci bashin naira miliyan 400 da sunan zai tayar da komadar kamfanin masaka ta Hirjira, amma shiru kake ji.

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Muhammad M Nami a matsayin sabon shugaban hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS, biyo bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Mista Babatunde Fowler.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel