Kotu ta bukaci a adana mata wani gwamna a gidan gyaran hali

Kotu ta bukaci a adana mata wani gwamna a gidan gyaran hali

Wani alkalin kotun majistare mai suna Douglas Ogoti, ya yankewa Gwamnan Nairobi, Mike Sonko zaman kwanaki biyu a gidan yari bayan da aka kamashi da laifin almundahanar kudade da cin hanci. An cafke gwamnan ne a ranar Juma’a, 6 ga watan Disamba 2019.

Gwamnan Kenyan ya gurfana ne a gaban kuliya a kan zarginsa da ake da laifuka sama da 30 da suka hada da almundahanar kudade, karbar cin hanci da kuma fada da hukuncin kotu. Ya amsa laifinsa bayan da aka kamashi da mukarrabanshi a kan wawurar makuden kudin da suka kai dala biliyan uku da rabi.

Kamar yadda rahoton ya nuna, bayanan asusun bankin Ogoti sun bayyana yadda ‘yan kwangila suka dinga tura masa kudade ta asusun bankinsa.

DUBA WANNAN: FIRS: Fowler ya gode wa Buhari, ya 'sace' gwuiwar masu cewa an cire shi

Sonko, wanda aka mayar zuwa gidan yarin Shimo la Tewa, an zargesa da tserewa a matsayinsa na dan fursuna. Ya roki kotun da ta bada belinsa saboda bukatar duba lafiyarsa bayan tserewar ‘wasan kwaikayon’ da yayi kafin kamashi a ranar Juma’a.

Daraktan gurfanarwa na ‘yan sandan kasar, ya soki bukatar belin Sonko. Ya yi nuni da cewa ya taba tserewa daga gidan yari. Ya kara da bukatar cewa, matukar aka bada belin Sonko, toh fa a dakatar dashi daga kujerarsa. Mai shari’a Ogoti zai yanke hukunci a kan wannan bukatar a ranar 11 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel