Tirka-tirka: Miji ya nemi matarshi ta kawo mishi buhun shinkafa 30, shanaye 6 da N52,000 kafin ya sake ta

Tirka-tirka: Miji ya nemi matarshi ta kawo mishi buhun shinkafa 30, shanaye 6 da N52,000 kafin ya sake ta

- Wani mutum mai suna Joel Lang'at dan asalin kasar Kenya ya bukaci buhunan shinkafa 30, Shanu 6 da wasu kudi daga wajen matarshi kafin sakinta

- An gano cewa, matar Lang ta maka shi gaban kuliya ne don rabuwa dashi, a yunkurinta na rub da ciki a kan sadaki da kayan auren 'yarsu

- Kafin nan, Lang da mai dakinshi sun taba rabuwa a shekarun baya inda ta yi shekaru 21 basu tare

Wani mutum mai suna Joel Lang'at dan asalin kasar Kenya mai shekaru 72 a duniya, ya bukaci buhunan shinkafa 30, shanu 6 da kudi har $146 kafin ya amince da warware aurenshi da matarshi.

Kamar yadda rahoton ya nuna, matar tana bukatar sakin da wuri ne sakamakon bikin 'yarsu da ke gabatowa, a yunkurinta na rub da ciki a kan sadaki da kayan auren.

An gano cewa, matar da mijin sun rabu kusan shekaru 21 da suka gabata, amma sai suka kara daura auren.

Kamar yadda matar ta ce, tana son a raba auren ne saboda cin zarafinta da mijin ke yi.

KU KARANTA: Sanna Marin: Budurwa ta farko da ta zama Firaiminista tana da shekara 34 a duniya

Ta ce: "Na bar gidanshi tun 1998. Mun rabu kusan shekaru 21 da suka gabata. Yakan bi ni da adda kuma wasu lokutan yana min barazana. Ban taba zama cikin kwanciyar hankali ba, don haka ne na tsere zuwa gidan iyayena.

A bangaren Lang kuwa, ya zargi matarshi da cin amana.

A kalamanshi: "Akwai lokacin da na taba kama matata da kwarto, amma da na fuskanceta sai ta gudu."

Bayan sauraron duk bangarorin biyu, alkalin ya dage sauraron shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel