FIRS: Fowler ya gode wa Buhari, ya 'sace' gwuiwar masu cewa an cire shi

FIRS: Fowler ya gode wa Buhari, ya 'sace' gwuiwar masu cewa an cire shi

Tunde Fowler, tsohon shugaban hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) da shugaban kasa ya sauya ranar Litinin, ya mika sakon godiya ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bisa bashi damar hidimtarwa kasa a karkashin gwamnatinsa.

Da yake gabatar da jawabin bankwana ga ma'aikatan FIRS jim kadan bayan sanar da nada sabon shugaban da zai maye gurbinsa, Fowler ya sace gwuiwar masu cewa an cire shi, saboda kawai shugaban kasa bai sake nada shi a karo na biyu ba.

Tsohon shugaban ya ce ba daidai bane ake cewa an cire shi, wa'adin zangonsa ne ya kare, kuma aka sake bawa wani dama ya dora daga inda ya tsaya kamar yadda shi ma aka nada shi bayan karewar wa'adin zangon wani shugaban.

Kazalika, ya kara da cewa, babu wani abu da zai dawwama ba tare da an samu canji ba koda kuwa jama'a basa son hakan.

Ya yi wadannan kalamai ne da misalin karfe 6:35 na yammacin ranar Litinin a yayin da yake mika mulki a hannun Abiodun Aina, darekta a hukumar FIRS mai kula da sashen harajin cikin gida.

Mista Fowler ya bayyana cewa ya san ya kawo sauye - sauye masu ma'ana da suka taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da al'amura a hukumar FIRS.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel