Yan ta'addan ISWAP sun yiwa Soji 2, dan sanda 1, yankan rago a sabuwar bidiyo

Yan ta'addan ISWAP sun yiwa Soji 2, dan sanda 1, yankan rago a sabuwar bidiyo

Wani sabon faifan bidiyo da ke nuna yadda aka kashe jami'an Sojin Najeriya biyu da dan sanda saya ya bayyana a yanar gizo. Channels Tv ta ruwaito.

Tsahar Channels ta bayyana cewa wasu mutane sanya da safar fuska da ake kyautata zaton yan ta'addan ISWAP ne suka yiwa jami'an tsaron yankan rago.

Rahotanni sun bayyana cewa ya ta'addan sun sace sojojin ne a BeniSheikh, wani kauye dake kilomita 70 da Maiduguri, jihar Borno.

Har yanzu ba'a san yawan Sojojin da aka sace ba amma bidiyon ya nuna mutane uku da aka daurewa hannu.

Gabanin kashesu, sai da jami'an tsaron suka gabatar da kansu tare da nuna katin aikinsu.

Amma har yanzu, hukumar Soji ko na yan sanda basu tabbatar da sunayen jami'an ba.

Daya daga cikin yan ta'addan ya yi jawabi a Hausa inda yayi barazana ga hukumar Sojojin Najeriya.

Ya bayyana cewa kungiyar zasu kai manyan hare-hare kan Sojoji.

Yace: "Muna kira ga Sojojin Najeirya, ba zamu ragawa masu yakan addinin Allah ba. Saboda haka sai mun kai muku hari barikin, wallahi sai min tareku a hanyoyi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel