Yadda wani sanata ya wawure kudin aikin mazabarsa ya gina otel - ICPC

Yadda wani sanata ya wawure kudin aikin mazabarsa ya gina otel - ICPC

- ICPC ta yi wata fallasa game da yanayin rashawar da ta yawaita a ‘yan majalisar tarayyar kasar nan

- Kwamishinan ICPC din na jihar Imo, Udonsi Arua, ya bayyana yadda wani sanata a jihar ya waskar da kudin aikin mazabu

- Arua ya ce, ya binciko tare da samo wasu kudaden aiyukan mazabu da aka waskar don amfanin kai

Daya daga cikin sanatocin da ke wakiltar jihar Imo a majalisar dattawan kasar nan, an zargesa da waskar da kudin aikin mazabarsa zuwa ginin otal din kansa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta yi wannan fallasar ne a ranar Litinin 9 ga watan Disamba.

Legit.ng ta gano cewa, kwamishinan ICPC din da jihar ke karkashinsa, Udonsi Arua, ya bayyana hakan ne a garin Owerri yayin bikin murnar ranar yaki da rashawa da majalisar dinkin duniya ta shirya na 2019.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Reinhard Bonnke

Ya kara da zargin cewa, wani dan majalisar tarayyar wanda ya siyo bas bas da a daidaita sahu a matsayin aikin mazabarsa, ya adana su ne gidansa ba tare da ya ba mutane ba.

A yayin jawabi a madadin shugaban ICPC din na kasa, Bolaji Owasanoye, Arua, ya bukaci ‘yan kasa da su hada kai da hukumar wajen yaki da rashawa, almubazzaranci da dukiyar gwamnati da kuma amfani da kujerar siyasa ta yadda bai dace ba.

Shugaban ICPC din ya bayyana yadda rashawa ke yin babbar illa ga ma’aikatun da ke fadin kasar nan. Rashawa na hana ingancin tsaro, kuma tana kawo kalubale a bangarori da daman a kasar nan.

Ya ce: “Abun tambaya a nan shine, mene ne ke kawo rashawa? Idan aka kokarta, akwai yuwuwar hada kai a kasar wajen yakarta?”

Ya ce, za a yi nasarar yaki da rashawa ne matukar aka yi kokarin fatattakarta a kowanne mataki na gwamnatin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel