Jaruman Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 37, sun kwato motocin yaki 4

Jaruman Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 37, sun kwato motocin yaki 4

Bayan irin gagarumin nasarorin da aka samu kan yan Boko Haram cikin makon da ya gabata, jaruman Sojojin Najeriya sun hallaka yan ta'adda 37 tare da kwato motocin yaki hudu a jihar Borno.

Harin da kwamandan Sakta 3 na Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Abdulmalik Bulama Biu, ya jagoranta, jaruman Sojin sun fitittiki yan ta'addan dake Duguri Arge,Tumbus, Karere, Gashigar, Arege, Metele, Malam fatori, da gefe-gefen tafkin Chadi.

PRNigeria ta tattaro cewa wannan hari da hukumar Soji ta kai na taron dangi ne.

Dakarun rundunar Operation Lafiya Dole, rundunar MNJTF da Sojojin kasar Chadi ne suna hada karfi da karfi wajen ragargazan yan ta'addan.

Hakazalika dakarun rundunar mayakan saman Operation Lafiya Dole sun taimakawa Sojin kasa da rahoton leken asiri.

Kalli bidiyon PRNigeria:

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel