Buhari zai ziyarci Masar tare da gwamnoni 3 da ministoci 2 a ranar Talata

Buhari zai ziyarci Masar tare da gwamnoni 3 da ministoci 2 a ranar Talata

A ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai bar Abuja zuwa birnin Aswan na kasar Masar (Egypt) domin halartar wani taro a kan tsaro da cigaban nahiyar Afrika.

Taron, wanda za a yi ranar 11 ga watan Disamba, 2019, zai tattauna a kan alakar da ke tsakanin zaman lafiya da cigaba a nahiyar Afrika da kuma yadda za a samar da hanyoyin karfafa dokokin da zasu tabbatar da tsaro tare da kawo cigaban kasashen nahiyar Afrika.

Shugaban kasar Misra, Abdel Fattah el-Sisi, ne ya bullo da shirin a matsayinsa na shugaban kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika (AU), sannan kuma mai rajin ganin an raya duk wani yanki da ya sha fama da rigingimu ko yake - yake.

Ana sa ran shugabannin kasashen nahiyar Afrika, shugabanni daga kungiyoyi da hukumomi na duniya, masana da kwararru daban-daban zasu halarci taron domin tattauna wa a kan damarmaki, fargaba da kalubalen da nahiyar Afrika ke fuskanta tare da samar da hanyoyin warware matsalolin kasashen Afrika.

Ana tsammanin cewa mahalarta taron zasu sake yin duba a kan shirin tare da mayar da shi wani sha'ani na shekara - shekara.

A ranar 28 ga watan Oktoba ne shugaban majalisar wakilan kasar Egyp, Ali Abdel Aal, ya ziyarci shugaba Buhari a Abuja domin isar da sakon shugaba el-Sisi na gayyatar shugaba Buhari zuwa wurin taron a watan Disamba.

Shugaba Buhari zai samu rakiyar gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, takwaransa na jihar Edo, Godwin Obaseki, da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Sauran ragowar 'yan tawagar shugaba Buhari sun hada da; Ministan tsaro, Bashir Magashi, karamin ministan harkokin kasashen ketare, Zubairu Dada, mai bawa shugaba kasa shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, da kuma babban darektan hukumar leken aisri ta kasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.

Ana sa ran cewa shugaba Buhari zai dawo Abuja ranar Juma'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel