Oshiomhole: Jerin Gwamnonin APC da matsayarsu a game da Shugaban Jam’iyya

Oshiomhole: Jerin Gwamnonin APC da matsayarsu a game da Shugaban Jam’iyya

Yayin da ake fama da rikicin cikin-gida a APC mai mulki, akwai gwamnonin da ke tare da shugaban jam’iyya na kasa, Adams Oshiomhole, akwai kuma wadanda ke neman ganin bayansa.

Mun kawo maku jerin gwamnonin jam’iyyar ta APC da inda su ka sa gaba a sabanin da aka samu.

Kamar yadda Jairar Daily Trust ta rahoto, Gwamnonin APC da su ke yunkurin ganin an sauke Adams Oshiomhole su ne:

1. Atiku Bagudu

Shugaban gwamnonin APC na Najeriya, Sanata Atiku Bagudu ya na cikin wadanda su ke hurowa Adams Oshiomhole wuta ya bar kujerarsa. Bagudu shi ne ya gaji Rochas Okorocha a kungiyar.

2. Nasir El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ba ya goyon bayan Adams Oshiomhole. Gwamnan ya na cikin wadanda su ke tare da tsohon shugaba John Oyegun a da, a karshe aka fi karfinsu a APC.

3. Simon Lalong

Shugaban gwamnonin na Arewa, Simon Bako Lalong ya na daga cikin wadanda ke tare da Tawagar Bagudu. Lalong ya na cikin jagororin gwamnoni ganin irin mukamin da ya ke kai.

4. Abubakar Sani Bello

Wani gwamna da ya ke cikin wadanda ke ganin cewa Adams Oshiomhole ba ya kokarin da ya dace a jam’iyyar shi ne gwamnan Neja. Abu Lolo ya na tare da Makwabtansa na yankin Arewa.

5. Godwin Obaseki

Mai girma Godwin Obaseki ya juyawa tsohon Mai gidansa baya. Rikicin Oshiomhole da Magajinsa ya yi karfi har ya gurbata majalisarEdo. Shi kadai ne gwamnan Kudu a cikin jerin.

KU KARANTA: Tsohon Gwamnan Arewa ya ce ba zai sake takara ba

Akwai gwamnonin da su ke tare da Adams Oshiomhole dari-bisa-dari, sun hada da:

1. Babagana Umara Zulum

2. Aminu Bello Masari

3. Abdullahi Umar Ganduje

4. Abdullaji Sule

5. Mai Mala Buni

6. Yahaya Bello

7. Babajide Sanwo-Olu

8. Dapo Abiodun

9. Gboyega Oyetola

Akwai wasu Gwamnonin da ba su nan ba su can. Kawo yanzu ba su fitar da matsayar su a cikin tafiyar ba. Su ne:

1. Rotimi Akeredolu

2. Kayode Fayemi

3. Muhammad Inuwa Yahaya

4. Badaru Abubakar

5. Abdulrahman Abdulrazaq

A na sa bangarem Shugaban kasa ya nuna cewa ya marawa Adams Oshiomhole bayan zama shugaban jam’iyya ne saboda irin kokarin da ya yi lokacin ya na kungiyar NLC da jihar Edo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel